Wani dalibin aji hudu da yake karatu a fannin koyon aikin likitanci a jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato, Kabiru Usman, ya zamo zakara a musabakar Al-Qur’ani ta maza da aka gudanar a Jihar Kebbi.
Kabiru Sani, wanda ya zo ta daya a rukunin masu haddar izifi sittin na Al-Qur’ani mai girma, ya samu kyautar Babur mai kafa uku.
- “Abin da ya sa nake yin daben ‘interlock’ da ledojin ruwa”
- Har yanzu El-Rufai bai fahimci batun matsalar rashin tsaro ba — Ganduje
- Dole sai mun yi sulhu da ’yan bindiga za a samu zaman lafiya — Matawalle
Haka kuma a rukunin mata da suka yi musabakar haddar izifi sittin, wata malamar makaranta, Hamida Bala ce ta zo ta daya wadda ita ma ta tashi da kyautar Babur mai kafa uku.
Da yake jawabi a wajen rufe gasar ranar Alhamis a Birnin Kebbi, gwamnan Jihar Abubakar Atiku Bagudu, ya ce akwai shirin da gwamnatinsa ke yi na kashe kimanin naira miliyan dari biyu da hamsin a Makarantun Islamiya na Jihar.
Ya ce kowace daya daga cikin zababbun makarantun Islamiya 504 za su samu akalla naira dubu dari biyar daga kudin da gwamnatin ta ware.
Bagudu wanda samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa Suleiman Muhammad Argungu, ya bayyana cewa kudin da gwamnatin ta ware za a kashe su ne wajen gyara da kuma samar da kayan aiki a makarantun.
Kazalika, ya ce daga cikin naira dubu dari biyar da aka ware domin makarantun, kowace makarantar za ta tashi da naira dubu dari yayin da ragowar kudin za a batar da su wajen gyare-gyare.
Yayin da yake yaba wa wadanda suka shirya musabar Al-Qur’anin da kuma taya murna ga wadanda suka yi nasara, ya ce wadanda za su wakilci Jihar a mataki na kasa da za a gudanar a Jihar Kano su dage wajen ganin an yi alfahari da su.