Dalibai sama da 90 da aka yi awon gaba da su a Kwalejin Tarayya da ke Yauri, Jihar Zamfara, sun yi Babbar Sallah a hannun ’yan bindiga.
Kusan mutum 100 da suka da dalibai da malamai ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kwalejin sama da wata daya ke nan yanzu.
Da farko dai wasu kalilan daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su din sun samu sun tsere daga hannun ’yan bindigar.
Da yake rokon Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ceto daliban, Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ngaski/Shanga/Yauri, Hon. Tanko Sununu, ya bukaci a kafa sansanin soji a yankin Masarautar Yauri domin samar da tsaro daga ’yan bindiga da ke kai musu hare-hare.
Ya ce duk da kokarin da gwamnati take yi domin kubutar da su, ya kamata ta kara dagewa domin a tseratar da daliban kwalejin da malamansu da wuri.
Dan majalisar ya ce harin da ya sa aka mayar da daliban kwalejin zuwa wata makaranta ya dagula lissafin daliban kwalejin da ke shirin rubuta jarabawar NECO, wadanda yanzu aka mayar da su wata makaranta inda kuma a can za su rubuta jarabawarsu.