✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban kwalejin Kogi sun yi zanga-zanga kan kisan abokansu

Daliban kwalejin koyon kimiya da fasaha ta jihar Kogi sun tare wani sashe na hanyar garin Lakwaja ta tashi daga garin Okene zuwa Lakwaja zuwa…

Daliban kwalejin koyon kimiya da fasaha ta jihar Kogi sun tare wani sashe na hanyar garin Lakwaja ta tashi daga garin Okene zuwa Lakwaja zuwa Abuja biyo bayan kisan da wata motar siminti ta yi wa abokanen karatunsu da wasu fasinjoji biyu.
Aminiya ta gano cewa wata motar gingimari dauke da siminti wacce take kan hanyarta daga garin Okene zuwa Abuja ta kwacewa direban ta yi karo da babur mai taya uku da kuma wata motar haya.
Wata daliba da ke karatu a sashen dakin kwaje-gwajen magunguna na kwalejin ta mutu tare da wasu fasinjoji biyu inda wasu mutum hudu suka samu munanan raunuka.
Jim kadan da aukuwar lamarin, sai dliban suka tare babbar hanyar da ke billewa kauyen Felele inda hakan ya janyo cunkoson abubuwan hawa har sai da jami’an kiyaye hadurra da sauran jami’an tsaro suka shiga tsakani sannan daliban suka amince a bude hanyar.