Daliban Jami’ar Abuja sun tare babbar hanyar zuwa filin tashi jirage na Abuja, inda suke gudanar da zanga-zanga kan karin kudin makaranta da jami’ar ta yi.
Kamfanin Dillacin Labarai NAN ya rawaito cewa, an hangi wasu daga cikin daliban yayin da suke zanga-zangar dauke da kwalaye da aka yi rubutu a jikinsu.
- Marayun Abuja sun kubuta daga hannun ’yan bindiga
- Za a rufe kasuwar Wuse da ke Abuja saboda karya dokar COVID-19
- Mutum 994 ne suka rasu a hadura a Abuja a 2020 —FRSC
- Rikicin #EndSARS: Makarantun Abuja na tura dalibai gida
Oladeja Olawale, shugaban Kungiyar Daliban Jami’ar (SUG), ya bayyana cewa sai an biya bukatunsu sannan za su daina zanga-zangar.
Ya kara da cewa dole ne a janye karin kudin makaranta da aka yi musu sannan a bude shafin rajistar Intanet na Jami’ar da aka rufe.
Olawale ya ce babbar hanyar da suka rufe ba za su bude ta ba matukar shugaban Jami’ar Farfesa Abdul-Rasheed Na-Allah, bai saurari kokensu ba.
Da yake jawabi kan zanga-zangar, kakakin jami’ar Habib Yakoob, ya ce za su zauna da daliban a teburin sulhu don nemo mafita.
Zanga-zangar dai ta kawo tsaiko ga masu ababen hawa, da sauran jama’a da ke amfani da wannan hanya.