Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya koka kan karuwar kingiyoyin asiri a Jihar, inda ya ce yanzu hatta daliban makarantun firamare sun fara shiga cikinsu.
Don haka Gwamnan yayi kira ga iyayen yaran da su kara mayar da hankali a bangaren walwakarsu, tare da tarbiyarsu domin kawo karshen annobar.
- Dan APC na so a hana Tinubu shiga takara saboda zargin yin karya a takardun karatunsa
- Cutar Kyandar Biri ta kama mutum 21 a Najeriya — NCDC
Gwamnan dai na wannan bayanan ne yayin bikin cika shekara 50 da samar da kungiyar Sagamites ta masu ruwa da tsakin garin Sagamu.
Kungiyar dai ta za ta kuma kaddamar da dakin taro na zamani a karshen mako.
To sai dai Gwamna Abiodun ya ce babu wani ci gaba da zai amfani muddin Jihar na cikin mummunan yanayin shigar yara kungiyoyin asirin.
Ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda ya ce daliban da ke rayuwa a gaban iyayensu ne ke shiga kungiyoyin asirin da haifar da rashin tsaro, ba wai fatalwa ba.