✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban FGC Yauri 2 sun tsere daga hannun ’yan bindiga

Daliban sun kubuta bayan kusan wata biyu a hannun masu garkuwa.

Biyu daga cikin daliban makarantar sakandaren kwana ta FCG Birnin Yauri da ke Jihar Zamfara da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su sun tsere daga hannun masu garkuwar.

Majiyarmu mai tushe ta ce daliban da suka tsere sun dauki tsawon lokaci suna tafiya a cikin daji ba su san inda suka nufa ba kafin su bulla a wani kauye da ke kusa da garin Dansadau a Jihar.

“Sun fada cikin wani gida ba tare da sanin inda suke ba. Da mazauna kauyen suka gane su sai suka boye su sai bayan faduwar rana aka kai su garin Dansadau aka ba wa DPO. Yanzu da nake maka magana ana hanyar  kai su Gusau,” a cewar majiyar.

Daliban na FCG Birnin Yauri sun samu tserewa ne bayan kusan wata biyu a cikin dajin da ’yan bindigar suka kai su bayan sun kwashe su daga makarantar inda suka kashe wani jami’in sanda kafin su dura yaran a mota su tafi da su.

“Ana zargin ’yan bindigar na tsare da daliban na FGC Birnin Yauri ne a Dajin Kuyanbana, da ya ratsa jihohin Zamfara da Kebbi da Kaduna da Katsina da kuma Neja,” inji majiyar.

Ta kara da cawa, “A cikin dajin ’yan bindiga suke boye mutanen da suka sace ko daga ina aka kawo su. Har wadanda aka yi garkuwa da su daga Kano a cikin dajin mai sansanonin ’yan bindiga ake kai su”.

Har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto ba mu iya samun karin bayani daga mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Zamfara, SP Muhammad ba.

A ranar 17 ga watan Yuni ne ’yan bindiga kutsa makarantar ta FGC Birin Yauri suka yi awon gaba da dalibai sama da 60.

Sace daliban shi ne karo na bakwai cikin wata shidan farkon 2021 da aka yi garkuwa da dalibai a Arewacin Najerya.