Jami’an ’Yan Sanda a Jihar Zamfara sun cafke wasu dalibai biyu da suka yi shirin sace ’yan uwansu dalibai a wata makarantar sakandare.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Hussaini Rabiu ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Juma’a a Gusau.
Ya ce an lamarin ya faru ne a unguwar Sha’iskawa da ke Gusau, babban birnin Jihar.
Ya ce, “Bayan samun da rahoton barazana, mun aike da jami’anmu kuma sun kama wadanda ake zargin wadanda ’yan ajin karshe ne a makarantar sakandare.
“Kazalika shugabar Kwalejin Anka ta bada rahoton ana mata barazanar sace dalibai idan bata bayar da kudi miliyan uku ba.
“’Yan sanda sun gudanar da bincike sannan sun kamo wani dalibi dan aji daya na babbar sakandare da ake zarginsu da hannu a ciki,” inji Kwamishinan.
Ya kuma ce rundunar ta sami nasarar cafke akalla mutum 45 da ke da hannu a tare babbar hanyar Gusau zuwa Sakkwato sau biyu cikin mako daya.
Ya ce an sami wadanda aka cafke din da yunkurin kone ababen hawan matafiya a kan hanyar, inda ya ce rundunar za ta mika su ga kotu da zarar sun kammala bincike.