✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban da suka rasa jarrabawar bana za su yi tasu ranar Asabar – JAMB

Kimanin dalibai 1,969 ne suka rasa jarrabawar a bana

Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta sanya ranar Asabar a matsayin ranar rubuta jarabawar cike gurbi ga wadanda ba su samu yin ta baya ba.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta shafin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya na Twitter ranar Alhamis

JAMB ta ce an shirya jarabawar ce domin wadanda wata matsala ta hana su rubuta jarabawar ta 2022 da aka yi a baya.

Idan za a iya tunawa, hukumar a baya ta ce fiye da dalibai 1,969 ne ba su samu zana jarbawar ta JAMB ba a bana.

Hakan ya faru ne sakamokon matsalolin daukar zanen yatsu da Lambar Tantancewar Banki (BVN) da sauran matsalolin na’ura da intanet.

JAMB ta kuma soke jarabawar cibiyoyi 10 da aka samu da karya dokokin jarrabawa a jihohi biyar.

Hukumar dai ta ce duk wanda ya fada wancan rukuni zai ziyarci shafinta a kan www.jamb.gov.ng, domin karin bayani.