Wasu daliban Kwalejin Ilimi a Jihar Kwara sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rashin biyan malamansu albashi har na tsawon lokaci.
Daliban mata da maza, sun kona tayoyi yayin da suke zagaye titin Ilorin, da sauran manyan titunan jihar, rike da alluna masu dauke da rubutu daban-daban da ke nuna suka a kan gazawar Hukumar Gudanarwar Kwalejin.
Zanga-zangar dai ta haifar da cushewar hanyoyi da dogayen layuka a manyan tituna, da kuma dakatar da zirga-zirgar masu tafiya a kafa.
Masu sayar da kayayyaki daban-daban ciki har da gidajen man da ke kusa da wurin, sun yi gaggawar rufe wuraren sana`o`insu, har sai bayan kammala zanga-zangar.
Shugaban Kungiyar Daliban Makarantar (SUG), ya ce sun yi zanga-zangar ne domin nuna goyon baya ga malamansu da ke cikin mawuyacin hali sakamakon rashin albashin.
Aminiya ta samu labarin cewa, Shugaban Kwalejin Dokta Jimoh Syinla-Agaka, ya jagoranci taro da Hukumar Gudanarwar Kwalejin domin lalubo yadda za a warware matsalar.