✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai sun yi wa ofishin gwamnan Kuros Riba kofar rago

Akalla dalibai 1,000 ne daga Jami’ar Kalaba da takwararorinsu na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kuros Riba suka yiwa manyan kofofin shiga ofishin gwamnan…

Akalla dalibai 1,000 ne daga Jami’ar Kalaba da takwararorinsu na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kuros Riba suka yiwa manyan kofofin shiga ofishin gwamnan jihar, Farfesa Ben Ayade kawanya na tsawon sa’o’i shida.

Matasan dai sun ce sun yi zaman dirshan ne a ofishin har sai an kawo karshen yajin aikin da Kungiyar Malam Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta shafe tsawon lokaci tana yi.

Da ya ke jawabi ga ‘yan jarida a ranar Litinin, shugaban Kungiyar Dalibai na Jami’ar Kalaba, Kwamared Raymond Moses  ya ce ba za su bar kowa ya shiga ko ya fita daga ofishin ba har sai gwamnan ko wani daga cikin mukarrabansa ya yi musu jawabi.

A cewarsa, “Mu dalibai muna cike da damuwa kuma mun fito ne a matsayin gargadi ga gwamnatin tarayya kan ta magance matsalolin dake tsakaninta da ASUU. Mun gaji da zama a gida.

“Ba inda za mu, mun yi zaman dirshan, kai a nan ma za mu kwana kuma gashi gwamnan ya ki fitowa ya saurare mu.

“Wannan zanga-zangar ta shafi ta kawo karshen rundunar SARS, ASUU da ma shugabancin mara inganci.

“Dukkan gwamnonin jihohi sun yi kunnen uwar shegu da halin da jami’o’inmu suka tsinci kansu.

“Kungiyar ASUU ta kasance cikin yajin aiki na kusan watanni bakwai da annobar COVID-19 ta kara ta’azzarawa, amma abin takaici kuulum sai bata lokaci suke kan tattaunawar da ta gaza haifar da da mai ido.

“Ana wasa da harkar iliminmu. Sun ajiye mu a gida, wanda hakan na daya daga cikin dalilan da suka sa muka fantsama kan tituna don mu huce takaicinmu.

“Ga kuma matsalar rashin tsaro ga yunwa, babu hanyoyin kyautatuwar rayuwa kwata-kwata,” inji shugaban daliban.

Sun ce suna neman gwamnan ya shiga tsakani wajen kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in.