Daliban Makarantar Glisten International Academy, Abuja, sun kirkiri butumbutumin da zai rika kai-kawo tsakanin likitoci da masu dauke da cutar COVID-19.
Mairabot, kamar yadda suka rada masa suna, zai taimaka wajen kai wa marasa lafiyar magani domin dakile kamuwar likoci da sauran ma’aikatan lafiya da cutar sakamakon mu’amallarsu da masu cutar.
- Mahara sun kashe babban jami’in dan sanda a Sakkwato
- An rusa Jabi Daki-Biyu bayan kwana biyu da gargadi
- Yadda matan Kano suka koma kasuwanci ta intanet
- El-Rufai ya ba Kannywood filin gina sinima a Kaduna
Shugaban Makarantar, Abba Abdullahi Saida, a bayaninsa lokacin da suka ziyarci Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa (NITDA) ya ce daliban sun samu kwarin gwiwar kirkirar na’urar ce saboda damuwarsu da yawan kamuwar ma’aikatan asibiti da COVID-19 a bakin aikinsu.
“An kirikire shi ne domin rage yawan hada jiki tsakanin malaman asibiti da marasa lafiya sannan zai matukar rage yawan masu kamuwa da cutar a yayin gudanar da aikinsu”, inji shi.
Ya kuma ce za su kula da matakan da ake bi wajen kirkire-kirkire a tabbatar za a iya amfani da Mairabot a ko’ina a fadin duniya, tare kuma da yin amfani da bashira wajen ganin ana amfani da shi a wasu bangarori na rayuwa.
NITDA za ta tallafa wa daliban
A jawabinsa, Shugaban NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, ya jinjina wa makarantar kan kirkirar na’urar.
Ya kuma bayyana aniyar taimaka wa masu kokarin kirkirar wani abu da zai magance duk wata matsala da ke damun kasa.
Abdullahi ya kuma yi kira ga daliban da su mayar da hankali kan hikimomin fasahar zamani domin can duniya ta dosa.
Sa’annan ya umarci bangaren kula da fasahar sadarwa da kasuwanci ya tabbatar da ba wadanda suka kirkiri na’urar kulawa har su kai ga fara sayar da shi a kasuwa.
Ya ba daliban da malaminsu kayan aikin fasahar zamani da za su taimaka musu wajen fadada tunanin da suke da shi.
Kayan sun hada da kwamfuta kirar IPad 6, da laptop 1 da sauran kayayyakin Intanet.