✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai mata sun yi wa maza fintinkau a Bauchi

Daga firamare har sakandare, ba inda mata ba su fi mazan kokari ba

Dalibai mata sun yi wa takwarorinsu maza fintinkau a jarabawar da aka gudanar a Jihar Bauchi.

Kwamishinan Ilimin Jihar Bauchi, Dokta Aliyu Tilde ne ya bayyana haka, ya kuma fede biri har wutsina kan yadda dalibai mata suka ba wa mazan mamaki a jarabawar makarantun firamare da sakandare a birnin Bauchi.

“Daya daga ciki shi ne dalibai mata sun fi takwarorinsu maza kokari a gwajin da aka yi na baya-bayan nan na ’yan aji shidan firamre da kuma gwajin jarabawar SSCE na ’yan ajin karshe na sakandare” inji a shafinsa na sada zumunta.

Kwamishinan Ilimin ya ce, “Ma’aikatarmu na ba da muhimmanci ga gwaji da jarabawar da ake yi; Abin da sakamakon ya nuna na da ban mamaki amma dole mu yi amfani da alkaluman yadda suke.”

Ya ce a jarabawar shiga aji daya a Makarantun Sakandaren Gwamnatin Tarayya na kwana 17 da ke Arewacin Najeriya, dalibai mata daga Jihar Bauchi sun zarce kason da aka ware musu.

“Mazan kuma dole muka yi musu rangwamen makin cin jarabawar don su cike ragowar gurabun; Karon farko da na taba ganin an rage wa dalibai maza yawan makin da ake bukata su ci jarabawa. Kai Jama’a!

“Abin bai tsaya haka ba, yayyansu —dalibai mata da ke SS3— sun yi wa mazan fintinkau a gwajin SSCE, musamman a Karamar Hukumar Bauchi wadda ita ce ke da mafi yawan dalibai maza a birnin jihar. A cikin dalibai 3,882 da suka yi nasara, 2,088  mata ne, maza kuma 1,794.”

A darajar makin da aka samu a gwajinma, matan sun nuna wa mazan cewa su ba kanwar lasa ba ce.

“Daga cikin masu ‘Distinction’ (A) 142 a Karamar Hukumar, mata ke da 91, maza kuma 51, sun kusa ninka mazan. A cikin B 719 kuma, matan ke da 544 mazan kuma 544. Matsakaicin daraja (C) kuma, mata na da 1,278 amma maza na da 1,199.”

Da aka sake rairayewa, an kara ganowa cewa makarantun matan sun fi na maza kokari, ba na kwanan ba, ballantana na je-ka-ka-dawo.

“A tsakanin manyan makarantun hadaka da ke garin Bauchi, ma haka take. A garin Bauchi, makarantar ’yan mata ta GGC Bauchi na da ‘Distinction’ tara, takwararta ta dalibai maza, Kwalejin Janar Hasan Usmna Katsina ba ta da ko ‘Distinction’ daya.”

A makarantun je-ka-ka-dawo ma, matan sun kara yi wa mazan kaye wajen yawan ‘Distinction’ kamar haka:

A Army Barracks, Mata 16, maza 8. Bakari Dukku kuma mata na da 20, maza 11; Dokta Ibrahim Tahir, mata 15, maza 10; Government Comprehensive kuam mata na da 7, maza 3.

A makarantar Birishin Fulani mata na da ‘Distincion’ 3, maza 1; Games Village kuma mata 3, maza 2; A Gwallemeji, mata 3, maza 3; sai kuma Saadu Zungun, mata 7, maza 2.

Sai dai ya ce a yankunan da ke wajen birnin Bauchi, samari ke kan gaba “suna cin moriyar al’ada da ta sa ilimin ’ya’ya mata ke koma baya.

“A wasu garuruwa irinsu Azare da Misauda makamantansu, gabalar da mazan suka samu a kan matan ba ta taka kara ta karya ba. Kare jini, biri jini aka yi.

“A kwalejin GCDSS Tilden Fulani da GDSS Gyamzo, duk a Karamar Hukumar Toro, dalibai mata da suka samu ‘Distinction’ sun ninka maza, sun kuma yi kunnen doki a GDSS Nabordo. ’Yan matan sun yunkura! A juri zuwa rafi!”

Cikin raha ya ce, shi kansa, “A ajinmu na karshe a jami’ar ABU a 1982, wanda ta fi kwazo wata yarinya ce ’yar Borno ne ce —ST—wadda ta taso a Legas. Duk da cewa yanzu shekara 39, na ki fadin sunanta kar ta zama tauraruwa shafina na Facebook! Ta hana mu rawar gaban hantsi.”

Yaya yanayin kwazon dalibai mata a wurare kama Kaduna, Sokoto, Kano, Maiduguri, Katsina, da sauransu yake? Tambayarsa ke nan.