✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibai fiye da 400 da suka karanci likitanci a ƙetare sun faɗi jarrabawar samun lasisi

Hukumar Kula da Kwarewar Likitoci ta Kasa MDCN ce ke shirya jarrabawar sau biyu duk shekara.

Akalla likitoci 433 daga cikin 836 da suka yi karatun likitanci a kasashen waje, sun faɗi jarrabawar samun lasisi, wadda Hukumar Kula da Kwarewar Likitoci ta Kasa MDCN ke shiryawa sau biyu duk shekara.

An dai gudanar da jarrabawar ce a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Dabo a ranakun 22 da 23 a wannan wata na Nuwamba.

Kazalika ta MDCN ta yi amfani da wasu cibiyoyin zana jarrabawar JAMB, inda ta gwada kwarewar wadanda suka kammala karatun likitancin a kasashen ketare.

An dai yi wa daliban jarrabawa kashi-kashi ciki har da ta tabbatar da kwarewarsu a fannin nazarin da suka yi karatu a kai da kuma ta tsarin na’ura mai kwakwalwa, inda sakamakon ya nuna fiye da rabi ba su yi nasara ba.

Rahotanni sun ce a kowacce shekara dalibai da dama kan samu guraben karatu a kasashen waje domin karanta likitancin, sai dai bayan sun dawo Nijeriya sukan fuskanci kalubalen cin jarrabawar samun lasisi.

Shugaban MDCN ta kasa, Dokta Tajuddeen Sanusi, ya ce suna shirya jarrabawar ce domin tabbatar da kwarewar mutum kafin barinsa ya fara gudanar da ayyukansa, kuma wannan tsari haka yake ko’ina a fadin duniya.