daruruwan jama’a daga kungiyoyin sa-kai hade da dalibai sun gudanar da zanga-zangar lumana a Ikko kan abin da suka kira rikon sakainar kashi da masu rike da madafan iko na Najerira ke yi wa harkokin ilimi, musammam ma da yake yanzu malaman jami’a suna yajin aiki kuma gwamnatin tarayya ta yi biris da al’amarin.
Masu zanga-zangar, wadanda suka kwashe sama da kilomita 20 suna tafiya da kafa suna kalaman sukar gwamnati dauke da kwalaye da ke da rubuce-rubuce kan haka, sun ce sun dinka wannan zanga-zangar ke nan har sai ranar da gwamnatin tarayya ta sake matsayi game da ilimi kuma ta saurare su.
Masu zanga-zangar dai sun tashi daga ofishin kungiyar kwadago ne zuwa ofishin gwamna, inda suka mika takardarsu wadda suka bukaci a mika wa Shugaba Jonathan. Gwamnatin Jihar Legas ta karbi wasikar tare da alkawarin za ta mika wa Shugaba Jonathan ba da jimawa ba.
Bayan sun bar ofishin gwamna ne kuma suka zarce dandalin marigayi Cif Gani Fawehinmi inda mutane daban-daban suka yi jawabin sosa rai game da harkokin ilimi a Najeriya, lamarin da ke hana ci gaba, kuma ana iya gyarawa kodayake an baro shiri can baya.
Kwamared Abiodun Aremu na kungiyar kare hakkin bil’adama ya ce abin da ya sa da yawancin mahukuntan kasar ke nuna halin ko-oho ga harkokin ilimi shi ne saboda ’ya’yansu ba sa karatu a cikin gida Najeriya, idan ma suna yi, sai ka taras makarantar kudi suke zuwa, don haka idan makarantun gwamnati sun sukurkuce ba abin da ya dame su.
Shi ma shugaban dalibai na jihohin Kuda maso Yamma, Kwamared Salami cewa ya yi ilimi da ya dace a ce yana sahun gaba wajen samun fifiko a kasafin kudin kasa, yau ya zame baya ga dangi. “Babban abin bakin cikin shi ne yadda gwamnati ke aiwatar da harkokin ilimi a takarda maimakon a aikace ya ce tun kafin malaman jami’a su fara yajin aikin sai da suka sanar da gwamnatin tarayya, amma sai ta yi biris da su kuma da suka fara, sun kwashe makonni, ba wanda ya ce musu uffan, sai surutai gwamnati ke yi ta kafofin yada labarai”. Inji shi.
dalibai da kungiyoyin sa-kai sun yi zanga-zanga kan tabarbarewar ilmi
daruruwan jama’a daga kungiyoyin sa-kai hade da dalibai sun gudanar da zanga-zangar lumana a Ikko kan abin da suka kira rikon sakainar kashi da masu …