Tsawon makonni kofar hanci da suka arce, na yi nufin gabatar wa ’yan makarantar Dodorido darasin Dakon-titin Sawun-wuya, da nufin caccakar uwar gidan Sawun-wuya, wanda ya yi fasakwaurin ’Yar bola zuwa kasar Hauwobiya, amma daga bisani na fasko cewa dara za ta ci gida. Domin mahukunta da talakawan Haurobiya duk dakon wuya suke yi; daga an tsallake wannan wahala, sia kuma a afka wata. Haurobiyawa kun ga an shashantar da batun Ciwon-cibin boko, saboda haka ta yi wu adon gari, sun shiga garari, ko ma sun salwanta.
Kaim jama’a! lallai adon gari sama da karamin lauje da sili da manuniyar sama sun yi batan dabo. Don haka kungiyar masu fafutikar shawo kan ciwon-cibin boko, har sun fara rankwafawa, domin sun gaji da dakon wuya. Hasali ma Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki a kasar Haurobiya, ya ce a daina yi wa fafutikar tazarcensa lakabi da “a dawo da shi karagar mulki a shekara ta dubu kramin lauje da sili da babban lauje.’ Haurobiyawa sai mu je, mu yi na damo, domin yamutsin Haramta Bobo da kwambon Bokoko ya dagula harkokin al’umma a Arewa maso Gabashin Haurobiya. Ita kuwa Gwamnatin Haurubja bat a damu da su ba.
Kai Haurobiyawa, ’yar bolar ma, Shagabannin Hurobiya sun ce ta daina yi musu Dodorido, don haka za a karkare hutun ’yan dugwi-dugwi, inda za su koma farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a tsakiyar watan Satin-Baba. Kai a daidai lokacin da nike kokarin bijiro muku da batutuwa kan dakon-titin sawun-wuya, a wato a ranar Tabawa ranar samu (inji mai bara), an shirya mana kwakwazon yaye duhun kai game da Yar bola, amma ban samu zuwa cikin lambun da aka shirya wannan shiri ba, don gudun kada a jefa ni lambatu, ni kuwa in yi ta batu a cikin bututu.
Haurobiyawa ana ta dakon wuya, domin wannan ita ce daddadar guguwar da aka alkawarta muku a matsayin gararumar jar miyar zabi tika a zabi sonka na shekara ta dubu karamin lauje da sili da sili. Shin ko ita ake son kwatawa, inda a wannan karon za a kara ruruta wutar Haramta Bobo da kwambon Bokoko; a hana manyan gobe koyon watsattsake da buda wagagen littattafai; a garkame kofofin shiga gidan Bokan Turai. Uwa-uba a tatuke lalitar ajiyar kasar waje, a dibga wa kasar Haurobiya dimbin lamuni, amma kullum ana ta baza cewa, ita ce kasar da ta fi kowace tarin dukiyar da ake hada-hada da ita a kasuwanci ko kuma wajen kason-wawanci, domin babu wani tasiri da dukiyar ta yi na warware dabaibayin talalar taluci da ya yi wa al’umma sasari.
To, mugunta fitsrin fako, wadanda ke kaunar Jam’iyya Mai dan boto da sanda jirge, sais u kara kaunarta, ta yadda za ta ci gaba da gasa wa al’umma aya a ka. Ku sani wannan jam’iyya mai mulkin mulaka’u, tana da kwararru masu shara zuki-ta-malle, kama kare ka hada shi da zomo. Ga Rubabben-Abban-titi da Mai karanta Labarun Mako a fadar Tsaunin Bila da Tonon-anini da Baudadden Joji da Aminin Dabo, har ma sun samu tallafin Shekararren mutumin nan na Jihar Tumbin-Giwa da Baffan-rawa na birnin Mujadaddi da sauran jiga-jigan jikata al’ummar Haurobiya.
Duk wanda ya baje na-zomo, ya kuma zuba na-mujiya, zai fasko irin tanade-tanaden da Mai dan boto ta yi na yamutsa Haurobiya, nan da shekara ta dubu karamin lauje da sili da baban lauje. Lokacin da jami’an kasar Uban-mama Jikan Kenyawa, jagoran Amurkawa suka yi has ashen tarwatsewar Haurobiya, kusan kowa caccakarsu ya rika yi, ashe ba a san cewa, Asarar-dan-kwabo da Tsoho Kilaki na nan sun jajirce, kan lallai sai dansu ya ci gaba da jan ragamar Haurobiya.
Sanin kowa ne akwai Kansakalin –kuku, wanda ya alkawarta wa Amurkawa cewa, da zarar an kawar da Jatau- mai sa-in-sa daga karaga, to za a ci aba da bumburutu buruntun satar mai a yankin Hauren-Danja.
Haurobiyawa, ni ban ga laifin uwargida Dakon-titi ba, da shiga shafin fuskantar bokoko, ta yi ta kare mai gidanta, wanda ya yi wo fasakwaurin ’yar bola cikin Haurobiya. Hakika talakawa da masu mulkin Haurobiya, ba su da kishi, shi yasa kasar nan ta zama lambatu, inda ‘’yar bola za ta shiga ta wataya.
Batu na ingarman karfen karafa, mu hada karfi wajen ganin mun samu jagoranci nagari. Mu rika gindaya sharudda ga masu laluben mukami, don kada su mayar da shi makamin make al’umma. Bisa wannan dalili, inda ganin wajibi ne idan wannan gwamanti ta jajirce kan cewa sai ta yi sabi zarce, to mu bukaci ta kawo mana maganin Ciwon-cibin-boko da rigakafin ’yar bola, sannan ta shawo kan yamutsin Haramta Bobo da kwambon Bokoko. Da zarar mahukuna sun nuna gazawa wajen sauke nauyin day arataya a kansu, to kowa sai ya yi daokon wuya, ko ma ya taka sawayensa har zuwa gidan wuya. Wuya ta kawo wa Haurobiyawa iya wuya.
A matsayina na Babban Direban Allin wannan farfajiya ta Dodorido, ina rokon Mai-duka ya yi mana katangar karfe da miyagun masu Bobo da kwambon Bokoko, kuma ya kashe mana wutar yamutsin Haramtata Bobo da kwambon Bokoko. Baya ga rokon da na gabatar a wajen Mai-duka, wajibi ne mu yi aiki na zahiri, wajen bayar da kowace irin gudunmuwa ga masu fafutikar ceton rayuka a yankin Arewa maso gabshin Haurobiya, musamman Jihohin Bararon-nono da Yawon-bebe, inda fitina ta lafe a dabe.
Dakon–titin Sawun-wuya
Tsawon makonni kofar hanci da suka arce, na yi nufin gabatar wa ’yan makarantar Dodorido darasin Dakon-titin Sawun-wuya, da nufin caccakar uwar gidan Sawun-wuya, wanda…