Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, ya ce Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Bubari, ya kyauta kan dakatar da ayyukan dandalin sadarwa na Twitter a kasar.
Shugaba Buhari ya dauki matakin ne bayan Twitter ya goge sakon da ya wallafa na yin kashedi ga masu neman tayar da rikici a kasar.
“Ina taya Najeriya murna bisa yadda Shugaban Kasar ya dakatar da Twitter a kwanan nan, ya kamata kasashe su yi koyi da shi wajen dakatar da Twitter da Facebook saboda suna hana bayyana ra’ayi — ya kamata a ji muryar kowane bangare,” inji sakon da Trump ya fitar.
Ya ci gaba da cewa, “Nan gaba abokan hamayyarsu za su bayyana su kuma yi karfi. Waye su (Twitter da Facebook) da za su ce su ne za su yi alkalanci kan abin kwarai da na tsiya, alhali su kansu abin tsiyar suke yi?
“Na so a ce na yi hakan lokacin da nake Shugaban Kasa, amma Zuckerberg ya yi ta kira na yana kawo min ziyara fadar While House yana min dadin baki cewa ni ne kankat. 2024?”
Trump ya yi bayanin ne kwana hudu bayan Facebook ya dakatar da shi na shekara biyu saboda samunsa da hannu a tunzura mutane su kawo hargitsi a Majalsiar Kasar Amurka, Capitol Hill.
Da farko Facebook ya dakatar da Trump sai abin da hali ya yi, saboda ikirarin da ya yi cewa shi ya kayar da Shugaba maici, Joe Biden a zaben kasar, lokacin Trump din na kan mulki.
A lokacin ne Trump ya bukaci magoya bayansa da su mamaye babban taron Majalisar Dokokin Amurka da zai tabbatar da nasarar Biden, mamayar da ta sa ’yan Majalisar tserewa.
A kan haka ne Facebook ya dakatar da Mista Trump, ranar Juma’a kuma ya sanar cewa tsohon shugaban ya cancanci hukunci mafi tsauri na saba ka’idojinsa.