Wasu mazauna Jihar Kano sun yaba wa Gwamnatin Tarayya kan matakin da ta dauka na dakatar da ayyukan shafin sada zumunta na Twitter a Najeriya.
Wasu daga cikin mazauna jihar da suka tattauna da Kamfanin Dillacin Labarai NAN a ranar Juma’a sun bayyana jin dadinsu game da hukuncin.
- Ma’aikatan kotu za su koma aiki makon gobe — Gwamnatin Tarayya
- Abin da ya sa beli kyauta ke zama ‘maganar ’yan sanda’
Wani dalibin Jami’a mai suna Yunusa Abdulkadir, ya bayyana dakatarwar a matsayin abin da ya dace.
Ya ce “Duk da ina yin bincike harkar karatu na da harkar kudaden Crypto da wasu abubuwa da suka shafi karatuna, amma na ji dadin dakatarwar.”
Wani Mista Usman Kabir, wanda ya ke amfani da shafin ya yi jinjina kan hukuncin da gwamnati ta dauka.
“Shafin ya tara mutane da ba su ganin girman mutane, suna wallafa sakonni na rashin da’a tun da babu doka a shafin.”
“Dakatarwar ta dauki lokaci, tun tuni ya kamata a dauki mataki saboda wasu marasa kishin kasa na kokarin ganin kasar ta balle.”
Sakina Habib, wata mai amfani da shafin ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda shafin ya goge sakon da Shugaba Buhari ya wallafa.
Ta ce “a yayin da wasu masu amfani da shafin da ke son kawo hargitsi a sun wallafa sakonni kuma suka sha ba tare da daukar mataki a kansu ba, amma sai shafin ya yanke shawarar goge sakon gargadin da aka wallafa don gujewa ballewar rikici a kasar.”
Kazalika, ta ce dakatarwar da aka yi wa shafin abu ne mai kyau musamman yadda aka yi maganin bata-garin shafin, duba da yadda shafin ke neman raba kan ’yan Najeriya.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ayyukan shafin zauren sada zumuntan a Najeriya cikin wata sanarwa da Ministan Labarai da Al’adu na Kasar, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a ranar Juma’a.