✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakarun Rasha sun shiga Ukraine da tankunan yaki

Putin ya umarci dakarun Rasha su shiga Ukraine da makaman yaki.

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewar an hangi tankunan yakin kasar Rasha sun fara sintiri a kasar.

A ranar Litinin ne shuagaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya bai wa dakarun sojin kasarsa umarnin shiga Ukraine don fara gudanar da yaki a tsakaninsu.

Tun bayan barkewar rikici tsakanin kasashen biyu da ke iyaka da juna, al’amura sun tsaya cak musamman a Ukraine.

Wannan ya sanya kasashen duniya, musamman Amurka suka tayar da jijiyoyin wuya don ganin Rashan ba ta mamaye Ukraine ba, sai dai hakan bai sa Putin ya yi kasa a gwiwa ba

Aminiya ta ruwaito cewa, shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke shiga tsakani tsamin dangartakar da ta kullu tsakanin Rasha da Amurka, ya shawarci bangarorin biyu su zauna a teburin sulhu domin dinke barakar da ke tsakaninsu.

Tuni dai Fadar Gwamnatin Amurka ta White House ta saka wa Rasha takunkumi kan mamaye yankunan Donetsk da Luhansk da ta yi a gabashin Ukraine.

Sanarwar daukar wannan mataki na zuwa ne sa’o’i bayan da Shugaba Vladimir Putin ya ayyana wadannan yankunan a matsayin masu cin gashin kansu.

Kazalika, mutane da dama da ke kasar Ukraine sun shiga damuwa kan abin da zai iya zuwa ya dawo, sakamakon kin aminta da tsagaita kai hari da Putin ya yi.