✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dakarun Najeriya sun kashe ’yan Boko Haram a Borno

’Yan Boko Haram hudu sun gamu da ajalinsu a hannun dakarun sojin Najeriya a kauyen Margummari da ke Jihar Borno. Dakarun Bataliya ta 22 da…

’Yan Boko Haram hudu sun gamu da ajalinsu a hannun dakarun sojin Najeriya a kauyen Margummari da ke Jihar Borno.

Dakarun Bataliya ta 22 da hadin gwiwar ’yan sa-kan CJTF sun kwato manyan bindigogi da albarusai da babura daga ’yan Boko Haram din da suka hallaka.

Daraktan Yada Labaran Rundunar Tsaro, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce: “Bayan samun bayanan sirri sojojin Bataliya ta 22 da ’yan CJFT sun kaddamar da sintiri a yankin Margumari.

“Ba su bata lokaci ba wurin bude wuta a kan ’yan Boko Haram din da ke kai-koma a yankin inda suka aika hudu daga cikinsu lahira.

“Sojojin sun kwato bindiga kirar FN daya da kuma AK-47 daya, sai kuma tarin kurtunan harsasai daga hannun ’yan ta’addan da suka cika bujensu da iska”, inji shi.

’Yan Boko Haram din suka debi kashinsu a hannu, “sun tsere sun bar albarusan 7.62mm kirar NATO, da wasu na musamman, baya ga babura da wayoyi da kayan kanikancin babura”, inji Onyeuko.

Ya kara da cewa sojojin Bataliya ta 444 da ke fatattakar ’yan Boko Hara a yankin Kirchinga da Shuwarin sun bindige karin dan kungiyar guda daya, wasu da suka samu raunin bindiga kuma suka sha da kyar.