Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) ta kashe ’yan ta’addan ISWAP sama da 25 tare da kwato makamansu a yankin Tafkin Chadi.
Sanarwar da kakakin rundunar, Laftanar-Kanar Kamarudden Adegoke, ya sanya wa hannu a N’Djamena ya ce dakarun Najeriya da Chadi sun samu nasarar ce bayan sun kai farmaki a yankin Tumbun Rago da Tumbun Dilla da Jamina a cikin yankin Tudun da ke cikin tsibiran Tafkin Chadi.
Ya ce sojojin sun kwato wani sansanin ISWAP inda suka kama wata mota mai dauke da bindiga makare da mai da kuma kakin soja da baburan Boko Haram guda 11 da injin ban ruwa guda biyu.
Laftanar-Kanar Kamarudden Adegoke ya kara da cewa bayan sojoji sun yi wa ’yan ta’addan luguden wuta, wadansu daga cikinsu sun tsere su bayar wani yaronsu mai shekara biyar, amma yana cikin koshin lafiya kuma za a mika shi ga hukumar da ta dace.
Ya bayayana yunkurin rundunar ta MNJTF na dakile barazanar ta’addanci a yankin tafkin Chadi na ci gaba da samun gagarumar nasara.
Ya ci gaba da cewa dakarun sun kama wani babban dan kungiyar ISWAP mai suna Musa Mani mai shekaru 43 a Damasak wanda ya amsa cewa ya gudu ne saboda tsananin hare-haren da suke fuskanta daga dakarun MNJTF.
Hakazalika, sojojin MNJTF daga kasar Kamaru sun kai farmaki ta ruwa da kan tudu a lokaci guda a kan mayakan ISWAP da suka mamaye al’ummar kogin Kirta Wulgo.
Sai dai ya ce abin takaici, wani mamba na Civillian JTF da ke tallafawa ayyukan MNJTF a Tumbun an halaka shi.
Sojojin Chadi da Nijar bakwai ne suka samu kananan raunuka kuma ana kai su a cibiyoyin soji daban-daban.
Kwamandan MNJTF, Manjo-Janar Abdul Khalifah Ibrahim ya jinjinawa jarumin da ya rasu, inda ya bayyana CJTF a matsayin jajirtattun matasa maza da mata wadanda suka bayar da gudunmawa sosai wajen yaki da ta’addanci.