Kamfanin Media Trust masu jaridar Daily Trust tare da hadin gwiwar Cibiyar Cigaban Dimokuradiyya (CDD), sun kaddamar da shafi na musamman don bincike da tantance sahihancin labara a intanet mai suna TrustCheck.
Babban Edita kuma Babban Darakta Daily Trust, Naziru Mikail Abubakar, ya ce an budde shafin TrustCheck, mai adiresehin trustcheck.dailytrust.com ne domin karfafa wa aiki da gaskiya da ci gaban dimokuradiyya.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin da ’yan Majalisa ke son CBN ya sassauta dokar cire kudi
- Mun saya wa ’yan banga kayan aikin N500m –Gwamnatin Neja
Ya ce Trustcheck aiki ne da Daily Trust ya sanya a gaba domin yaki da yada labaran karya a cikin al’umma.
Haka nan, sahen talabijin na kamfanin (Trust TV) na gabatar da shiri na musamman na minti 15 duk ranar Juma’a domin fadakar da al’umma kan sha’anin yaki da labaran bogi.
A cewar Naziru, jami’an da aka dora wa wannan aiki za su rika aiki bakin kokarinsu wajen taimaka wa masu bibiyar kafafen yada labarai na Media Trust domin samun sahihan labarai a kodayaushe.
Don haka ya ce, masu sha’awa na iya ajiye adireshinsu na imel ta: trustcheck.dailytrust.com domin samun sakonnin tatattun rahotanni da sauran labarai kowace Alhamis.
Kamfanin ya ce nan ba da dadewa ba za a samar da makancin wannan shafin a harshen Hausa don amfanin masu mu’amala da harshen.
A nata bangaren, Daraktan CDD, Idayat Hassan, ta ce “Muna matukar farin cikin yin wannan aikin tare da Daily Trust.”
Ta ce wannan shi ne irin abin da ake bukata a Najeriya duba da yadda labaran karya suke yi wa cigaban harkar dimokuradiyya tanarki.