✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dage dokar kulle a Borno: Me zai biyo baya?

Bayan da hukumomi a jihar Borno suka dage dokar zaman kulle suka kuma ba da damar bude wuraren ibada, masana sun gargadi jama’a da su…

Bayan da hukumomi a jihar Borno suka dage dokar zaman kulle suka kuma ba da damar bude wuraren ibada, masana sun gargadi jama’a da su kara kiyayewa da matakan kare kai daga kamuwa da coronavirus.

Dokta Muhammad Bukar wani Masani ne a kan kiwon lafiyar al’umma a Maiduguri da ya ce ya ji dadin dage dokar, amma kuma akwai abin dubawa.

“Jama’a su sani cewa wannan cuta gaskiya ce, kuma su kasance masu bin duk wani umarni da aka bayar don kare kai daga kamuwa da cutar”, inji shi.

Masana da dama dai sun yi gargadin cewa janye dokar ka iya mayar da hannun agogo baya a yunkurin kawar da annobar ta COVID-19.

A yi hattara

Shugaban Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Yammacin Afirka, Farfesa Abdulsalam Nasidi, na cikin wadanda ke ganin barin dokar ya fi janye ta.

“Idan alal misali cutar za ta kashe mutane 1,000, idan aka hakura aka zauna a gida, barazanar mutuwar na iya raguwa zuwa mutane dari kacal”, in ji Farfesa Nasidi.

Dokta Bukar ya ce kiwon lafiya abu ne mai muhimmanci ga jama’a, don haka ya jaddada bukatar jama’a su kula da wanke hannu a-kai-a-kai da amfani da takunkumin rufe fuska idan za su shiga jama’a da kuma kauce wa cunkoso; sannan ya yi kira ga al’ummar jihar Borno su dage da addu’a don Allah ya kawo karshen cutar.

Wannan ne ma dalilin da ya sa malaman addini suka nuna farin ciki da dage dokar saboda hakan zai ba mutane damar yin ibada.

Damar yin addu’a

Limamin Farin Masallaci na Galadima Alhaji Abubakar Ali ya dage dokar “zai bai wa jama’a damar gudanar da ibadunsu, musamman a wannan [kwanaki] na karshe [a watan Ramadan].

“Zai bai wa jama’a damar rokon Allah Ya kawo mana karshen ita wannan cuta, kuma muna godewa Gwamna Zulum a kan wannan karamci da ya yi mana na bude gari don jama’a su sami abinci”.

Limamin ya kuma yi kira ga ’yan kasuwa da su ji tsoron Allah su tausaya a wannan wata, sannan ya bukaci al’umma da su kasance masu bin dokoki don kare kai daga kamuwa da coronavirus.

Ra’ayoyin mutanen gari

Wakilin Aminiya ya tattauna da wasu jama’ar gari, don jin ra’ayoyinsu a kan dage wannan doka.

Wani matashi mazaunin Maiduguri, Sheriff Adam Balum, ya ce ya yi farin ciki da aka dage dokar.

“Hakika hakan zai bai wa jama’a damar su fita domin neman abinci tun da akasarin jama’armu talakawa ne da sai sun fita suke samun abin da za su ci da iyalansu, to amma a gaskiya akwai matsala domin an bayyana cewar cutar ba ta son cunkoso.

“Dole ne mutanenmu za su hadu a yi cunkoso, kuma ni na yarda cewa cutar nan gaskiya ce, don haka ina shawartar mutanenmu da su bi hanyoyin kariya da aka tanadar don gudun kamuwa da ita”, inji shi.

Shi ma Babagana Bukar cewa ya yi gaskiya yana mutukar farin ciki da aka dage wannan doka da ta takurawa al’umma.

“Kai ka san yadda jama’armu suke masu karamin karfi ne, wanda sai an fita, za a samu abin da za a sa a bakin salati.

“Kuma ni tun da na tashi ban taba gani an hana mu sallar jumma’a ba, sai a wannan lokaci – duk rikicin Boko Haram ba mu daina sallar jumma’a ba, to kaga a yanzu abin farin ciki ne, kuma kira na ga mutane mu kasance masu bin ka’idojin da aka shimfida don kare kai daga kamuwa da coronavirus”.

A ranar 22 ga watan da ya gabata ne dai gwamnatin jihar Borno ta kafa dokar hana fita ta tsawon mako biyu, wadda bayan karewar wa’adin ne aka kara mako guda, duk da nufin hana cutar coronavirus yaduwa.