✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dagaci ya rasa rawaninsa a Kano saboda badakalar filaye

Tuni dai Sarkin ya ba da umarnin nada sabon Dagacin da zai maye gurbin shi

Masarautar Gaya a Jihar Kano, ta tsige Dagacin kauyen Gudduba da ke yankin Karamar Hukumar Ajingi a Jihar, Malam Usman Muhammad Lawan.

Sarkin Gaya, Dokta Aliyu Ibrahim Abdulkadir ne da kansa ya ba da sanarwar tsigewar, wadda ta soma aiki nan take.

Ya ce an tsige Dagacin ne bayan da aka same shi da hannu dumu-dumu cikin badakalar filaye.

Tuni Masarautar ta Gaya ta bukaci Hakimin yankin, Alhaji Wada Aliyu, (Madakin Gaya) ya tura sunan wanda za a maye gurbin korarren Dagacin da shi.

Sarkin ya yi gargadin cewa Masarautarsa ba za ta lamunci duk wani rashin da’ar da zai taba mutuncinta ba.

Daga nan, ya shawarci duka masu sarauta na Masarautar da su yi riko da gaskiya dangane da mukaman da aka ba su.