✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daga ƙasashen waje Boko Haram ke samun makamai da kuɗaɗe —Shugaban sojoji

’Yan Boko Haram sama da 120,000 sun miƙa wuya, galibinsu kuma an same su da kuɗaɗen manyan ƙasashen duniya. Ta ina suke samun kuɗaɗen, wa…

Najeriya ta bukaci Majalisar Ɗinkin Duniya da ta binciki hanyoyin samun horo da kuɗaɗe ’yan ta’addan Boko Haram da suka shafe shekara 16 suna addabar ƙasar.

Babban Hafsan Tsaro Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya yi wannan kiran a wata hira da kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ta yi da shi kan matsalar tsaro a ƙasar.

Janar Christopher Musa ya wanda ya ɗora ayar tambaya kan yadda ayyukan suka ci gaba a tsawon shekara 16 duk da yadda sojoji ragargajarnsu, ya yi zargin maƙarƙashiyar ƙasashen duniya wajen sama wa kungiyar kuɗaɗe da horo da kuma makamai.

Ya ce aka akasarin mayaƙan Boko Haram da sojoji ke kamawa ana samun su ɗauke da kuɗaɗen manyan ƙasashen duniya, wanda hakan ke nuna alamar ƙasashen duniya na da hannu wajen ƙulla maƙarƙashiya da ayyukan ƙungiyar.

Ya kuma buƙaci Majalisar duniya su yi bincike kan sabuwar dabarar da ƙungiyar ta ɓullo da ita ta amfani da jirage marasa matuƙa wajen yin leƙen asiri karin su kai wa jami’an tsaro hari.

Da yake amsa tambaya kan dalilin da mayaƙan Boko Haram ke sake taruwa su kai hare-hare bayan sojoji sun yi iƙirarin murƙushe su, Janar Christopher Mustapha, ya ce ya yi zargin akwai kuɗaɗen da ƙasashen duniya ke ba wa ’yan ta’addar, yana mai neman Majalisar Ɗinkin Duniya ta shigo domin gano masu hannu a daukar nauyin ’yan ta’addan.

Ya ce ya kamata “Yanzu haka sama da ‘’yan Boko Haram 120,000 ne suka miƙa wuya, kuma akasarinsu mun samu su da kuɗaɗen manyan ƙasashen duniya. Wa ya ba su? Ta ina suke samun kuɗaɗen ƙasashen? Wa ke ba su horon? Ta ina suka sami makaman?

“Majalisar Dinkin Duniya na bukatar shigowa saboda a gano tushen kuɗaɗen. Ai harkar hadahadar kuɗaɗen ƙasa da ƙasa ne kuma ba mu da iko kan hakan, ”in ji shi.

Game da abin da yake zargi, Janar Christopher Musa ya ce, “ba za a rasa haɗin bakin ƙasashen duniya duniya ba… Yaya aka yi Boko Haram suka ci gaba da ayyukansu da ɗaukar nauyin kansu tsawon shekaru goma sha biyar? Wannan abin tambaya ne.

Sai dai ya bayyana cewa ba shi da masaniyar kasashen da ke neman hana Najeriya zama lafiya, duk da cewa ba ita ce kaɗai ƙasar da ke fama da ’yan tayar da kayar baya ba, a yankin Sahel da ma Afirka ta Yamma.