Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce akwai yiwuwar hadakar Jam’iyyar APC za ta rushe bayan shan kaye a zaben 2023.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana haka ne jim kadan bayan kaddamar da bangaren matasa na kwamitin yakin neman zabensa ranar Alhamis a Abuja.
- An gurfanar da wani mutum a kotu kan satar tayar babur
- 2023: Gwamna Buni ya gabatar da kasafin N163.2bn
Aminiya ta rawaito gamayyar jam’iyyu uku ne suka hadu suka samar da APC da suka hada da jam’iyyar ACN karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu da CPC karkashin Janar Muhammadu Buhari, sai kuma jam’iyyar ANPP da wani bangare na APGA da kuma sabuwar PDP.
Atiku ya ce kasancewar PDP tsohuwar jam’iyya wannan ya sa take da kwarewar da za ta iya rike dimokuradiyyar Najeriya yadda ya kamata.
“Magana ta gaskiya, PDP ce jam’iyya daya tilo da ta tsaya da kafarta a kasar nan. APC hadaka ce tsakanin CPC da jam’iyyar Tinubu.
“Za mu kayar da su a wajen zabe sannan za su mutu murus. Ba na tunanin za su ci gaba da kasancewa bayan Zaben 2023,” in ji Atiku.
A nasa bangaren, abokin takarar Atiku kuma Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya ce, Najeriya na cikin wani hali a hannun APC wanda tana bukatar wadanda za su ceto ta.