✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DAGA LARABA: Yadda ‘Sakacin Ma’aikata’ Ke Lakume Rayuka A Asibitin Murtala

Dalilan zargin jami'an lafiya da yin watsi da marasa lafiya a Asibitin Kwararru na Muratala da ke Kano.

More Podcasts

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

Zargin sakaci da rayukan marasa lafiya, musamman mata masu ciki a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano ya karade kafafen sadarwa a ’yan kwanakin nan.

Ana zargin yadda ma’aikatan asibitin ke nuna halin ko-in-kula da rayukan jama’a na sanadiyyar mutuwar mata da jarirari kusan kowace rana.

Shin me ya sa asibitin Murtala ya yi kaurin suna haka a wurin jama’a?

Shirin Daga Laraba ya tattauna masu korafi kan asibitin da kuma masu fafutukan kawo gyara.