More Podcasts
Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa.
Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa.
Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni ta yadda shugabanci zai riƙa kewaya a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan bai samu shiga ba a Majalisar Wakilai.
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO
- DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan wannan tsari na karba-karba da tasirinsa.
Domin sauke shirin, latsa nan