Majalisar Dattawa ta fara muhawara kan kudurin dokar mulkin karba-karba tsakanin shiyyoyin siyasar Najeriya.
A farkon shekarar 2022 da muke ciki ne Majalisar ta kammala karatu na farko kan kudurin dokar wanda Sanata Abba Moro a gabatar.
- Yau ce ranar fara yakin neman zaben 2023 a Najeriya
- Duk da tabbacin Buhari, Fasinjoijn jirgin kasa sun yi wata 6 a tsare
Wannnu batu na neman yin dokar mulkin karba-karba dai ya janyo ce-ce-ku-ce, kamar yadda batun mulkin karba-karba ya jima yana tayar da kura a fagen siyasar Najeriya.
Wasu ’yan Majalisar Dattawa na ganin dokar za ta bai wa al’ummomi, musamman marasa rinjaye damar shiga a dama da su a fagen shugabancin kasar nan.
Wasu takwarorinsu kuma na zargin kafa dokar za ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.
A lokacin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bukaci wanda ya gabatar da kudurin da ya janye ta, ya je ya yi masa kwaskwarima sannan ya sake gabatar wa majalisar.