More Podcasts
Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren Larabci wato Almuhajir, da ke nufin wanda ya bar garinsa don zuwa wani gari neman ilimi.
Mafi yawan al’ummar Arewa inda aka fi amfani da kalmar almajiri, sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da Musulunci ya fara shigowa Najeriya daga garin Maidugurin Jihar Borno zuwa kasar Hausa.
- NAJERIYA A YAU: Shin addu’oi kaɗai Najeriya ke buƙata dom ficewa daga matsaloli?
- DAGA LARABA: Adawar Gwamnonin Arewa da Ƙudurin Haraji: Kishin Ƙasa Ko Son Zuciya?
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi duba ne a kan tarihin almajirci da kuma yadda yake a da can baya.
Domin sauke shirin, latsa nan