✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabid Beckham ya sayi hannun jari a kulob din Salford City

Rahotannin sun ce shahararren dan kwallon Ingila da kulob din Manchester United Dabid Beckham ya mallaki hannun jari a kulob din Salford City da ke…

Rahotannin sun ce shahararren dan kwallon Ingila da kulob din Manchester United Dabid Beckham ya mallaki hannun jari a kulob din Salford City da ke Ingila. Kulob din dai yana wasa ne a rukunin ’yan dagaji.

Rahoton da kafar watsa labarai ta UK Sun ta kalato a shekaranjiya Laraba ya nuna cewa Beckham ya shiga sahun tsofaffin ’yan kwallon Manchester United na 1992 irin su Ryan Giggs da Paul Scholes da Gary Nebille da Phil Nebille da suka mallaki kashi 60 daga cikin 100 na hannun jari a kulob din.

Rahoton ya nuna Beckham ya sayi kashi 10 daga cikin 100 na hannun jarin ne da hakan ta sa tsofaffin ’yan kwallon United din suka mallaki kashi 60 daga cikin 100 na kulob din.

Shahararren dan kasuwa, dan asalin Singapore Peter Lim ne ya mallaki ragowar kashi 40 na hannun jari a kulob din na Salford City.

Sai dai kafin yanzu Beckham ne ya mallaki kulob din Inter Miami da ke Amurka da ake sa ran zai fara wasa a gasar rukuni-rukuni na Amurka da aka fi sani da Major League Soccer a badi idan Allah Ya kai mu.