✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dabarun kiwon kifi na Gwamnatin Kano zai taimaka wa al’umma’

An bayyana fadada bada horo kan dabarun kiwon kifi da Gwamnatin Jihar Kano take yi a matsayin abin da zai kara dogaro da kai tsakanin…

An bayyana fadada bada horo kan dabarun kiwon kifi da Gwamnatin Jihar Kano take yi a matsayin abin da zai kara dogaro da kai tsakanin al’umma maza da mata.

Hajiya Hauwa Jar Dawa Funtuwa daya daga cikin matan yankin Karaduwa da ke Jihar Katsina da ta samu horo kan dabarun kiwon kifi a makarantar koyar da dabarun kiwon kifi ta Kano da ke Bagauda ce, ta bayyana hakan a garin Funtuwa a ranar Talata lokacin da suka gayyaci Daraktan Makarantar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, domin nuna godiyar su ga gwamnatin Jihar Kano kan manufofinta na samar da sanao’i ga al’umma don su dogaro da kansu.
Ta ce abubuwa sun yi wa gwamnatoci yawa wajibi ne a rika bullo da hanyoyin samar da ayyukan yi ga al’umma, ta yadda za a rage dogaro da gwamnati wajen samun aikin yi, musamman a wannan zamani da muke ciki.
Jagoran al’ummar yankin Karaduwa, Alhaji Haruna Abdulrasheed, kuma tsohon kakakin karamar Hukumar Funtuwa ya ce, gwamnatin Jihar Kano ta yi fice kan al’amuran da suka shafi samar da sana’oi ga al’umma ta hanyar kirkiro da hanyoyin bada horo ga al’umma, inda hakan ya sanya ake samun dogaro da kai da karuwar arziki a jihar.
Ya yaba bisa yadda ake zakulo dalibai daga sauran jihohin kasar nan, ana ba su horo kan dabarun kiwon kifi domin kara inganta rayuwar al’umma.
Ya ce “Wannan tsari na samar da sana’oi ba tare da nuna bambanci ba abin a yaba ne.”
Daraktan makarantar horar da dabarun kiwon kifi na Jihar Kano, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya gode wa al’ummar yankin Karaduwa saboda gayyatar sa da suka yi, domin su yi godiya bisa abin da gwamnatin Jihar Kano ta yi masu na horar da al’ummarsu.
“Da yardar Allah za a kara bullo da sabbin hanyoyin inganta rayuwar al’umma wajen ba su horo kan sana’oi daban-daban, ta yadda zamantakewa za ta yi dadi. A yanzu gwamnatin Jihar Kano tana da tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikin al’umma ta fannoni masu yawa.” Inji shi.