Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf , ya ce Najeriya na fuskantar manyan matsaloli da dama da ke buƙatar dabaru domin magance su.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su kasance masu kishin ƙasa domin tabbatar da samun gobe mai kyau.
- Zan rantse da Alƙur’ani ban saci kuɗin Kaduna ba — El-Rufai
- Zanga-zanga: An jibge jami’an tsaro a hanyar gidan gwamntin Gombe
Ya yi wannan kira ne a lokacin bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar.
Gwamnan ya ce, “Yayin da muke tunawa da gudummawar shugabanninmu na baya, ya kamata mu yi tunanin abin da za mu iya yi don ci gaban wannan jiha mai girma. Ta yaya za mu tabbatar da cewa hidimar da iyayenmu suka yi ba ta tafi a banza ba? Mu yi fatan alheri, haɗin kai, da kuma tafiya a kan manufa guda ɗaya.
“Mu koyi darasi daga nasarorinmu na baya da ƙalubalen da muka fuskanta, mu fuskanci rayuwar gaba da jarumta. Tare, za mu iya shawo kan kowace irin matsala, mu cimma burinmu, kuma mu ciyar da ƙasar nan gaba.
“A yau, a bayyane yake cewa muna fuskantar matsaloli da dama. Daga matsalolin tattalin arziƙi zuwa rashin daidaito a zamantakewa, batun tsaro har zuwa tasirin sauyin yanayi, muna fuskantar ƙalubale da ke buƙatar hanyoyi masu ƙarfi da ƙirƙire-ƙirƙire.
“Duk da haka, ba za mu bari waɗannan matsaloli su dakatar da mu daga ƙoƙarin gina kyakkyawar makoma ga kowa a Jihar Kano da Najeriya ba.”
Gwamna Yusuf, ya kuma yi fatan samun kyakkyawar makoma, sai dai ya jaddada cewa hakan zai dogara ne da yadda mutane za su haɗa kai, kamar yadda shugabanni baya suka yi.
“Dole ne mu haɗa kai ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, ƙabilanci, da addini ba don fuskantar manyan matsalolin da muke fuskanta.
“Kowannenmu yana da rawar da zai taka, ko kai shugaba ne na gargajiya, shugaba na addini, ma’aikacin gwamnati, manomi, malami, dalibi, ko ɗan kasuwa.
“Ta hanyar aiki tare, bayar da gudunmawa ga al’ummarmu, da kuma bibiyar shugabanni kan abin da suka yi, za mu tabbatar da cewa an samar da ƙasa mai ƙarfi, daidaito, da kuma tsayuwa fiyw da yamma muka same ta.”
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali kan aiwatar da ayyukan da za su amfani al’umma da kuma bunƙasa jihar.
“Za mu ci gaba da yin aiki tuƙuru don inganta rayuwar mutanenmu, haɓaka ci gaban kowa da kowa, da kuma gina al’umma inda kowa zai iya cika burinsa kuma ya bayar da gudunmawa mai tasiri ga ci gabanmu baki ɗaya,” in ji shi.