Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU), ta yi kira da dalibai ’yan aji uku da ajin karshe a jami’o’i da su himmatu da yin bita a gida ba tare da sun kosa ba.
ASUU ta ce akwai yiyuwar nan take a fara jarabawa da zarar aka bude makarantun idan suka daidaita da Gwamnatin Tarayya.
- ASUU na zargin Akanta Janar na kasa da mallakar kadarorin biliyoyin Naira
- EFCC: Kwamitin binciken Magu ya kai wa Buhari rahoto
- EFCC: Kwamitin binciken Magu ya kai wa Buhari rahoto
Kungiyar ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter ‘yan sa’o’i kafin ci gaba da zaman tattaunawarta da Gwamnatin Tarayya.
Idan ba a manta ba ASUU ta kwashe kusan wata takwas tana yajin aiki sabonda rashin samun daidaito da gwamnati kan bukatun ’ya’yanta.
A ranar Juma’a ake sa ran kungiyar za ta kuma zama a teburin sulhu da wakilan gwamnati a ofishin Ministan Kwadago, Chris Ngige.