✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da zan samu na kammala rubuta littafina da burina ya cika- Bashir Tofa, a hirarsa ta karshe

Ya ce wannan littafin ya tsaya masa a rai matuka.

Tsohon dan takarar Shugabancin Kasar a Jamhuriya ta uku, marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa ya bayyana cewa da zai samu ya kammala rubuta wani littafi da ya sanya a gaba, to da burinsa na rayuwa ya gama cika.

Marigayin ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da Jaridar Aminiya a gidansa kwanaki kadan kafin rasuwarsa.

Marigayin ya ce duk da cewa ya rubuta litattafai masu yawa, amma littafi ne ya tsaya masa a gaba saboda rashin kammaluwarsa

“Zuwa yanzu na rubuta litattafai 14 wadanda kuma na buga su. Amma a yanzu akwai littafin da nake rubutawa mai suna ‘Mutane da wurare a duniyar Islama’.

“Ina shafi na 740. Abin da nake yi shi ne ina dauko sunayen mutane da suka yi rayuwa a wurare daban-daban a duniyar Musulunci. Ina bincike a wasu litattafaina ina zakulo sunayen mutanen.

“Yadda na tsara littafin na biyo jerin haruffan A, B, C, D ne, yanzu dai ina kan harafin U. Insha Allah na kusa kammalawa.

“Wannan littafi ya tsaya min a rai saboda na gaza kammala shi,” inji marigayi Bashir Tofa.

Marigayin ya bayyana cewa a duk lokacin da rashin lafiya ta kama shi yakan shiga fargaba kan yiyuwar rashin kammaluwar littafin.

“A koyaushe na ji rashin lafiya ta kama ni sai na ce shi ke nan ba zan kammala littafi na ba ke nan. Wallahi kullum rokon Allah nake ya bar ni na kammala rubuta wannan littafin.”

Idan har na kammala rubuta wannan littafin to ni fa burina ya cika. Ko da na tafi shi ke nan. Ni wallahi shi kadai nake jira na kammala.”

Marigayin ya bayyana cewa ba wai dabi’ar son karatu ne ke hana mutane karatu ba illa rashin kudin sayen littafi.

Ya kuma ce, “Ni a tunanina mutane suna son karatu sai dai ba su da kudin sayen littafi, wanda hakan shi yake hana su yin karatu. Ga litattafan nan na buga da yake an yi bugu mai kyau da inganci sai ya zama ya gagari mutane. Shi ya sa ma yawanci kyauta nake raba litattafaina kyauta. A duk lokacin da na tashi raba litattafan haka za ku ga mutane sun cika wurin.”

Alhaji Bashir Tofa marubucin Adabin Hausa ne a ya rubuta litattafai a suka hada da Kammaninka Tunaninka, da Kimiyyar Sararin Samaniya da Rayuwa Bayan Mutuwa da daI sauransu.

Ku kasance da Aminiya ta ranar Juma’a mai zuwa don karanta cikakkiyar hirar!