Majiyoyi masu tushe sun sanar da cewa Sevilla ta shirya sake kulla yarjejeniyar shekara biyar da dan wasan baya na kungiyar Real Madrid, Sergio Ramos.
A shekarar 2005 ce Ramos ya dawo Real Madrid daga Sevilla inda ya murza leda a ajin matasa.
A yanzu Ramos wanda shi ne kyaftin a Madrid ya shafe tsawon shekaru 16 yana haskawa inda ya lashe dukkan wasu kofuna na gasannin da kungiyar ta buga.
A yanzu dai ana ci gaba da cece-kuce kan makomarsa yayin da kwataraginsa da kungiyar zai kare a karshen wannan wata na Yuni.
Sai dai a ranar Juma’ar da ta gabata ce rahotanni daga Sfaniya suka bayyana cewa, Ramos zai yi wata muhimmiyar tattaunawa da Shugaban Real Madrid, Florentino Perez, dangane da makomarsa a kungiyar.
Sai dai har ya zuwa wannan lokacin, babu wani tabbaci dangane da yadda tattaunarwarsu ta kare, inda da dama ke ganin Ramos zai san inda dare ya yi masa a ranar 1 ga watan Yuli.