✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da wuya Gareth Bale ya buga wasan Madrid da Tottenham – Zidane

Kocin Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya bayyana shakku a kan dan kwallon  gabansa Gareth Bale inda ya ce da wuya ne dan kwallon…

Kocin Real Madrid na Sifen Zinedine Zidane ya bayyana shakku a kan dan kwallon  gabansa Gareth Bale inda ya ce da wuya ne dan kwallon ya iya buga wasan Madrid da Tottenham na Ingila  a ranar Laraba 1 ga watan Nuwamban 2017 a Gasar cin kofin zakarun kulob na Turai.  Wasan zai gudana ne a Ingila kuma a wasan farko kungiyoyin biyu sun yi kunnen doki ne da ci 1-1 a Sifen.

Bale wanda ya ji ciwo tun a wasan da Madrid ta yi da kulob din Borussia Dortmund na Jamus kimanin wata daya da ya gabata, da wuya in zai murmure a kan lokaci har ya buga wasan da ake ganin zai yi zafi.

Bale dai tsohon dan kwallon Tottenham ne, kuma magoya bayan kulob din Madrid za su so ganin dan kwallon ya buga wannan wasa ganin yadda  kungiyoyin biyu ke fafutukar samun nasara a wasan.

Raunin da ya ji ne ta sa bai yi wa kasarsa Wales wasa ba a kokarin hayewa gasar cin kofin duniya da hakan ya sa kasar ta rasa gurbin tafiya gasar da za ta gudana a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu.

Gareth Bale dai yana shan suka a wajen magoya bayan Madrid da kuma mahukunta kulob din musamman ganin yadda yake yawan jin rauni.  Hakan ta sa wasu suka rika yin kiraye-kirayen a sayar da shi kafin ko a karshen kakar wasa ta bana.