Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar nan a Jihar Kano da ake zargi da kisan dalibar nan mai shekara biyar, Hanifa, ya ce da shinkafar bera ta N100 ya yi amfani wajen kasheta.
Wanda ake zargin dai shi ne mai makarantar Noble Kids da ke Kano, kuma ya kashe yarinyar ne bayan ya sace ta, sannan ya yi yunkurin karbar kudin fansa daga iyayenta.
- Manyan makaman ’yan sanda 178,459 sun yi batar dabo
- Kotu ta yanke wa barawon kaza hukuncin daurin shekara daya
Aminiya ta rawaito cewa tun farkon watan Disamban bara ne aka sace Hanifa lokacin da take kan hanyar komawa gida daga makarantar Islamiyya.
Malamin dai ya bukaci a biya shi Naira miliyan shida a matsayin kudin fansarta, inda a wajen karbar kudin ne dubunsa ta cika.
Sai dai ko a lokacin da yake kokarin karbar kudin fansar ma ya riga ya hallaka ta, amma ya ki shaida wa iyayenta.
To sai dai bayan kama shi, wanda ake zargin ya shaida wa ’yan jarida a hedkwatar ’yan sandan Kano ranar Juma’a cewa da shinkafar bera na N100 ya yi amfani wajen kashe yarinyar.
Rahotanni sun nuna cewa malamin dai ya daddatsa Hanifa bayan ya kasheta, sannan ya binne ta a cikin makarantar.
Tuni dai Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin a gaggauta rufe makarantar har sai abin da hali ya yi.