Malam Umar Sani Mai Kwarya magidanci ne da ke sana’ar sayar da kore a Kasuwar Shanu ta Iseyi a Jihar Oyo, yake kuma samar da kore a lungu da sakon jihar.
Ya shaida wa Aminiya cewa da sana’ar ya auri mata hudu, yake kula da su da ’ya’yansu 11 cikin rufin asiri, ya kuma mallaki gidan da yake zaune da iyalan nasa a Jihar Oyo.
Malam Umar dan asalin Gummi a Jihar Zamfara ya ce, “Da sana’ar sayar kore nake duk wata dawaniyata da ta iyali da kuma ’yan uwa da abokan arziki.
“Daga ita na fadada zuwa wasu sana’o’i masu alaka da ita kamar sayar da turmi, rariya, kuka da sana’ar sayar da shinkafa.
“Yanzu haka ina da yara da dama da suke zuwa suna daukar kaya a wajena suna zagayawa da su lungu da sako suna samun abun kansu muna karuwa da juna”, inji shi.
Ya ce ko da yake yanzu zamani ne na amfani da robobi amma hakan bai hana shi samun ciniki yadda ya kamata ba, domin har yanzu ana amfani da su ta hanyoyi daban-daban.
“Fulani na saya su zuba nonon shanu ko fura da makamantan haka, sannan wasu na saya su jika magani.
“Muna sayar da karamar kwarya…muna sayar da luddai da faifan rufe kwarya, babu abun da zan ce ga wannan sana’a sai dai na yi wa Allah godiya”, inji shi.
A karshe Malam Umar Mai Kwarya ya yi kira ga matasa da su rike sana’a komai kankantanta, domin su dogara da kansu.