Dan wasan gaba a kulob din Bayern Munich Frank Ribery ya bayyana cewa saboda farin cikin lashe kofin gasar zakarun kulob-kulob na Turai da kulob dinsa na Bayern Munich da ke Jamus ya yi a makon jiya ta sa ya dauki kofin zuwa gidansa inda ya kwana da shi a rungume yayin da matarsa ke gefe.
A wasan karshe da kulob din ya yi da na Borussia Dortmund a ranar Asabar ta makon jiya an tashi wasan ne Bayern ta samu nasara da ci 2-1.
Kimanin sau uku kenan kulob din Bayern yake kai wa ga wasan karshe a gasar a cikin shekaru hudu da suka gabata amma sai a wannan karon ya samu nasarar lashe kofin a karo na biyar a tarihin gasar.
A lokacin da yake bayyana farin cikinsa ga manema labarai yadda al’amarin ya faru, Frank Ribery ya ce “Na rungume kofin da muka lashe a kan gadona, ma’ana na kwana da shi a rungume kuma saboda dadin barci ban farka ba sai kusan karfe shida na safe”. Abin mamaki matata tana gefe ni kuma ina gefe rungume da kofin don ji nake tamkar kofin ya fi ta mahimmanci a wannan lokaci saboda murna”.
Shi dai Frank Ribery yana daga cikin zaratan ’yan kwallon Bayern Munich kuma tuni ya sake sabunta kwantaraginsa a kulob din.
Da kofin zakarun kulob-kulob na Turai na kwana -Frank Ribery
Dan wasan gaba a kulob din Bayern Munich Frank Ribery ya bayyana cewa saboda farin cikin lashe kofin gasar zakarun kulob-kulob na Turai da kulob…