✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da kai ne Al-mustapha, za ka yafe wa wadan su ka zalunceka?4

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya…

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya koma gida, bayan daurin da aka yi masa na tsawon shekara kusan 15. Ana zargin wasu ne suka yi masa makarkashiya da kazafi. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan a ce kai ne Al-mustapha, ko za ka iya yafe wa wadanda suka yi sanadiyyar jefa ka cikin wannan ukuba? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka bayyana dangane da haka:

Zan iya yafewa – Ibrahim Muhammad
Ibrahim Muhammad: “Idan ni ne Al-mustapha, zan yafe domin kuwa babu abin da ya fi yafiya alheri. Idan muka duba, za mu ga cewa yafiya halin Annabi (SAW) ce kuma ya yi umarni da a yi yafiya. Duk da irin abin da aka yi wa Al-mustapha kuwa, wannan kaddara ce kuma nufi ne na Ubangiji kuma jarrabawa ce. Mun san cewa idan aka cuci
mutum yana da zabi ko ya yafe ko kada ya yafe, daga bisani Ubangiji zai bi masa hakkinsa. Amma kuma duk da hakan yafewa ce ta fi, domin mun ga cewa ita Annabi ya zaba kuma ya fifita ta a kan mutum ya rama.”