✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da ka tsaya da na fasa maka kai da shantu

  Wani kwarto ne ya je gidan abokiyar harkarsa, kwarto na leka dakin matar ta taga ya hange ta kan gado, yana matsawa sai ya…

 

Wani kwarto ne ya je gidan abokiyar harkarsa, kwarto na leka dakin matar ta taga ya hange ta kan gado, yana matsawa sai ya bugi tiren kwanuka, maigida na ban daki, sai ya rugo da gudu su ka yi arba da kwarto. Kwarto ya ranta a na-kare mai gida ya bi shi da katon abu a hannunsa. Suna cikin gudu sai maigidan ya ce “Da ka tsaya da na faffasa maka kai da wannan shantu!” Koda kwarto ya ji ashe shantu ne a hannun maigidan sai ya tsaya ya ce: “Da ma shantu ne a hannunka, nake ta gudu kamar raina zai fita!” Sai kwarto ya juyo kan maigida, ganin haka maigida ya juya da gudu da kyar ya kai gida da gudu da roron wake.
Daga 09099886988