Lawan Ibrahim Natamadina, Kasuwar Waya wani mai gyaran takalma ne a babbar kasuwar garin Gombe wanda ya share sama da shekara 40 yana wannan sana’a kuma ya ce ta rufa masa asiri domin har ya gina gida albarkacinta.
Ya ce tun yana da shekara bakwai ya koyi wannan sana’a kuma zuwa yanzu ya koya wa yara fiye da 20.
“Na fara gudanar da wannan sana’a ne tun zamanin mulkin Janar Murtala Muhammad a tsohuwar Kasuwar Gombe kafin ta tashi ta koma sabuwar kasuwa, har yanzu haka kuma wannan sana’a ita na rike kuma ita ce gatata,” inji shi.
Har ila yau, ya ce, “Ba ni da wata kalma da ta wuce gode wa Allah kullum a kan wannan sana’a saboda ba karamin rufin asiri ne a cikinta ba, domin albarkacinta ne na mallaki gida na yi aure.”
Ya kara da cewa cikin yaran da ya koya wa wannan sana’a ta gyaran takalma yanzu haka wasu har motocin hawa suke da su.
Daga nan ya yi kira ga matasa cewa su daina zaman banza su nemi sana’a komai kankantarta saboda za ta rufa musu asiri “Domin idan mutum ya rike sana’a ba maganar karamar sana’a domin ta fi yawon maula a tsakanin ’yan siyasa balle ma uwa uba zaman banza,”inji shi.
Da gyaran takalma na gina gida –Lawan Natamadina
Lawan Ibrahim Natamadina, Kasuwar Waya wani mai gyaran takalma ne a babbar kasuwar garin Gombe wanda ya share sama da shekara 40 yana wannan sana’a…