Na yi wata rashin lafiya mai tsanani na zazzabi da zubar jini ta hanci. Aka kai ni asibiti aka yi gwaje-gwaje aka ce ina da ciwon SLE. Da na tambaye su don su mini bayani sai suka ce na je na bincika, shi ne nake neman karin bayani ta wannan kafa.
Daga Murja, Kano
Amsa: E, kwarai kuwa akwai ciwo mai suna SLE a likitance, sai dai ban san sunansa da Hausa ba, amma tabbas wani nau’i ne na borin jini mai karfin gaske, wanda ake shan maganin rage karfinsa har sai illa-masha-Allahu. Ya kamata a san cewa cutukan borin jini su ne suka fi kowadanne irin nau’ukan ciwo yawa a tsakanin ’yan Adam, domin an san fiye da dari, cikinsu kuwa har da wasu nau’ukan cutukan daji da nau’in ciwon suga na matasa da sauransu. Wato kusan dai a ce wasu kwayoyin halittu na jikinmu su ne manyan masu kawo mana cutuka, ba abinci ba, ba kwayoyin cuta ba.
Wasu da yawa suna faruwa ne haka kawai ba dalili, wasu kuma da ma sun gaji matsalar, wasu kuma sai sun shiga wani hali na matsi, kamar na canjin yanayi, ko na canjin abinci, ko na ruwa, ko cizon wasu kwari, da ma sauran abubuwa da za su sa jiki ya ga canji na wahala farat daya. Idan mutum ya yi sa’a wadannan kananan halittu na jikinsa ba masu bori ba ne, to kusan zai iya zama lafiya, domin akwai wadanda kowane irin hali suka samu kansu a ciki jikinsu, ba ya nunawa.
Wasu nau’ukan borin jini marasa tsanani sukan yi sauki cikin mintuna, kamar wanda sinadaran wasu kwari masu cizo kan sa; wasu cikin ’yan kwanaki, kamar cin wani nau’i na abinci da jiki kan gani a matsayin bakon abinci; wasu kuma sai an yi makonni suke lafawa. Wasu sai an dan sha magani na ’yan kwanaki, wasu kuma ba ma sai an sha ba da kansu suke lafawa. Misalan sauran cutukan borin jini masu karfi irin wannan su ne masu kama gabobin jiki wato ciwon sanyin kashi na ‘arthritis’ da kuma masu iya kama sauran sassan jiki kamar hanta, ko koda, ko makoko da sauransu. Inda wannan ciwo ya fi sauran karfi shi ne na cewa shi ko’ina a jiki zai iya lahantawa.
Shi wannan ciwo na SLE yana daya cikin cutukan da kan faru idan kwayoyin garkuwar jiki suka rikice suka fara yakar jiki maimakon cuta, wanda shi ne borin jini. Mun riga mun san kwayoyin garkuwar jiki kamata ya yi a ce su zauna jiran shigowar kwayoyin cuta, idan sun shigo jiki su yake su. To haka kawai kuma, a wasu lokuta, sukan rikice su yaki jiki, kamar dai misalin a samu sojojin wata kasa su yi tawaye, wasu akan magance tawayen cikin kwanaki, wasu cikin watanni, wasu bayan shekaru, kai wasu ma sukan yi sanadiyar ruguza kasar.
Shi wannan ciwo an kiyasta cewa ya fi kama bakaken fata, mata da maza, amma mafi yawa a mata ya fi ta’azzara, musamman masu kiba. Alamun ciwon sun danganta da inda kwayoyin suka fara tabawa a jikin mutum. Kusan kowa mai wannan ciwo yana samun zazzabi mai tsanani na makonni wanda zai ki tafiya. Sa’anna kin ce naki ya zo da habo, alamar ke nan ciwon ya fara yakar kananan kwayoyin jini na ‘platelets’ masu sa jini dan dankon nan da yake da shi, wanda idan babu su ko yaya mutum ya ji ciwo sai jini ya yi ta zuba ko a fili ko a karkashin fata. Sauran alamun sun hada da ciwon gabobi idan ya fara taba gabobin jiki ke nan. Idan ya taba koda kuma akan fara ganin ko fitsarin jini ko kumburin jiki ko dai wasu alamu na ciwon koda; idan ya taba fata akan ga wasu kuraje wadanda suka fi yawa a fuska da kirji. Hasali ma wadannan kuraje na fuska wadanda suke fitowa a kan kumatu da hanci da goshi su ne babbar alamar ciwon wanda da an gan su ba tantama. Sauran alamun sukan ta’allaka ne a kan sauran bangarorin jiki da ciwon ya tabo.
Ana gano ciwon da sauri idan aka yi gwaje-gwajen da suka dace. A gwaje-gwajen ne akan ga kwayoyin kare garkuwar jiki wato fararen kwayoyin jini sun yi yawa sosai, na jajayen kwayoyin jini da ‘platelets’ kuma sun yi kasa sosai. Sa’annan a jinin dai, har ila yau, akan auna wasu sinadarai da suke nuni da borin jini kamar A.N.A da kika yi bayani, ‘Rh Factor’ da kuma masu nuna takamaimai ciwon SLE irin su ‘Anti dsDNA’ (wadanda ma watakil sai an kai jinin wata kasa kafin a gwada) da sauransu. Idan aka gwada fitsari ma ana ganin wasu sinadaran da bai kamata a gani a fitsari ba. A wadannan gwaje-gwajen na jini da fitsari kawai, ana iya gano matsalar, sai a jini kawai za a iya bukatar gwaje-gwaje da suka kai goma ma.
Magunguna, kamar yadda na fada, tun da fari ana shan su ne kullum kusan har sai inda karfi ya kare, sai dai idan an ga karfin ciwon ya rage akan rage wasu. A wasu kalilan idan aka ci sa’a aka tsaida magunguna shi ke nan jikin sai ya zauna lafiya. A wasu kuma sai abin ya dawo. Magunguna ne kala-kala kuma wasu ma masu tsada da ake amfani da su wajen rage karfin wadannan kwayoyin halittu masu yakar jiki. Sai dai akan yi taka-tsantsan, tunda akan rage karfin kwayoyin garkuwar jiki, kwayoyin cuta ke nan sukan yi saurin shiga jikin mutum su kawo wani ciwon na daban. Shi ya sa ake ba da wasu magungunan kuma na riga-kafin kwayoyin cuta, akan kuma ba da shawarawarin kiyaye kamuwa da kwayoyin cuta ta hanyar tsabtar jiki (musamman hannaye), abinci, ruwa, da makamantasu.
Sauran matsalolin magungunan kuma su ne irin matsalolin da akan samu idan an sha su. Akwai masu sa kiba, idan an dade ana amfani da su; akwai masu sa zubewar suma; akwai masu rikita al’ada ga mata; akwai ma masu iya hana ma daukar juna biyu.
LAFIYAR MATA DA YARA
Amsoshin Tambayoyi
Ni mahaifata ce ta kumbura na je asibitin garinmu aka ce sai an min wani gwaji na ‘Pap smear’. An dauka yanzu an kai babban asibiti za a gwada. An ce sai bayan mako biyu zai fito shi ne nake neman karin bayani.
Daga Maman Ruma, Yobe
Amsa: A’a, tunda ana jiran sakamako ai kin ga likitocinki ke nan ba su kai ga gano matsalar taki ba, idan ma har akwai, ballantana ni. Kada mu riga Malam Masallaci, ki hakura ki yi ta addu’a gwaji ya fito lafiya. Shi ‘Pap smear’ gwaji ne da ke nufin za a karanta kwayoyin halittu na bakin mahaifa a ga me ya sa mahaifar take ba ki wadannan alamun da kike ji.
Wai me ke kawo ciwon mara ga mai juna biyu?
Daga Binta M., Zaria
Amsa: Shi juna biyu kansa zai iya kawo ciwon mara ko da ba wata matsala. In dai babu wasu alamu kamar zubar jini, zazzabi, amai da ire-irensu kuma kin je awo, an auna an dau hoto an ce komai zanzan, ai kin ga ba a ce matsala ba ce, motsi ne da mahaifa kan yi. Akan samu irin wannan, musamman a farko-farkon cikin da karshe-karshensa. Idan yana tsanani a karshe-karshen ciki kuma ba zubar jini ko wasu alamu, to yana nuni ne da farawar nakuda.
Idan ina al’ada sai cikina ya rika kullewa duk bayan mintuna biyar, sa’annan ya saki shi ne nake neman shawara.
Daga Fauziyya
Amsa: Ke ma a iya cewa in dai har wannan matsala sai kina al’ada ne kawai take zuwa, to ba abin tashin hankali ba ne. Da ma wasu matan ai sukan samu wannan matsala, wanda shi ma motsi da kullewar naman jikin mahaifa kan jawo, amma kuma matsalar ba ta da magani sai dai masu dan sa sauki kamar panadol, feldene, da sauransu. Wasu da sun haihu sun warke ke nan, wasu kuma ko sun haihu, idan al’adar ta dawo ciwon ya dawo ke nan.
Idan ya rage min mako guda na yi al’ada, na fara ciwon baya ke nan da kafa da kugu da mara da mama, kai duk rikicewa ma nake na rika razana, shi ne nake tambaya ko wata matala ce.
Daga Maman Al’amin Hausawa
Amsa: Wannan duk aikin sinadaran da mahaifarki da dangoginta kan saki ne dab da al’ada. Ba ciwo ba ne, da ma na wasu ya fi na wasu.
karin bayani: Wasu matan sa ce ita dai wannan mahaifa ta faye matsaloli. kwarai kuwa haka ne, mahaifa da dangoginta, kamar kwan ‘obaries’ da sinadaran ‘hormones’ da suke fitarwa sun fi komai jawo ciwo a mata. Abin da wasu matan ke yi idan suka ga mahaifar na ta damunsu da matsaloli shi ne: bayan sun tabbatar haihuwar ’ya’ya ta ishe su kuma sun tattauna da maigidansu, kawai asibiti suke zuwa a cire ta ko tana da ciwo ko ba ta da ciwo, ko sun daina al’ada ko ba su daina ba. Da yawa-yawan matan sun ce sun fi jin sakat bayan an rage ta kuma ba abin da ya ragu a rayuwarsu. Sinadaran da take fitarwa akwai wasu sassan jiki da ke fitar da kadan irinsu.