✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar Shan-inna ta sake bulla a Jihohi 13 da Abuja

A bara dai WHO ta ba Najeriya shaidar fatattakar cutar daga kasarta.

Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA) ta ce ya zuwa ranar Litinin, Najeriya ta sami rahoton bullar sabon nau’in cutar Shan-inna wacce ake kira da cVDPV a Jihohi 13 da Babban Bairnin Tarayya Abuja.

Jihohin sun hada da Abiya da Bayelsa da Borno da Delta da Jigawa da Kano da Kebbi da Legas da Neja da Ribas da Sakkwato da Yobe da Zamfara da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Babban Daraktan hukumar, Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin yayin taron hukumar da masu rike da sarautun gargajiya daga Arewacin Najeriya na zango na biyu na 2021.

A bara dai hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba Najeriya shaidar fatattakar cutar daga kasarta.

Masana dai sun ce ba kasafai ake samun yaduwar cutar ba, ko da yake ta rika karuwa a ’yan shekarun nan sakamakon karancin yin allurar rigakafinta yadda ya kamata.

Faisal, wanda Dokta Usman Adamu na hukumar ya wakilta ya ce NPHCDA ta gudanar da bincike a kan cutar nau’in NOPV har karo hudu, wanda ya ce shine mafi tasiri a yaki da cutar.

Ya ce, “An sami bullar cutar ne sakamakon kaucewa yin rigakafinta da wasu iyalan suka rika yi, wanda hakan kuma zai yi matukar illa ga yunkurinmu na dakile ta baki daya.”

Shugaban ya kuma koka kan cewa yawan tallafin da kungiyoyi da hukumomi ke bayarwa wajen yaki da cutar ya ragu matuka.

Daga nan sai ya yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya da su kara zage damtse wajen janyo hankulan ’yan siyasa wajen bukatar ci gaba da ware kudade don yaki da ita.

Shima da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Masu Rike da Sarautun Gargajiya Da ke Kula da Lafiya a Matakin Farko kuma sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad ya yi alkawarin cewa zasu ci gaba da goyon bayan dukkan shirye-shiryen da Gwamnatin Tarayya za ta bullo da su wajen yaki da cutar, matukar bai fi karfinsu ba.