Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce an sami rahoton bullar cutar murar tsuntsaye nau’in H5N1 a jihohi bakwai na Najeriya.
Jihohin sun hada da Kano da Bauchi da Filato da Gombe da Nasarawa da Kaduna da kuma Neja.
- Dan Majalisar Wakilai, Suleiman Lere ya rasu
- Ma’aikatan shari’a sun garkame kotuna bayan fara yajin aiki
Babban Daraktan hukumar, Dakta Chikwe Ihekweazu ne ya sanar da hakan yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata a kan yanayin cututtuka a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa dai cutar wacce asalinta tsuntsaye da kaji ta fi kamawa za ta iya kama mutane ma.
Yawanci dai ana kamuwa da cutar ne idan mutum ya yi mu’amala da tsuntsun da ya kamu da cutar kuma kwayoyin cutar su kan bi iska ne yayin da za a iya daukarsu ta hanyar tari ko atishawa.
Babban Daraktan ya ce alamomin da aka fi gani a jikin wanda cutar ta kama sun yi kama da alamomin sanya kamar tari, zazzabi, bushewar makogwaro, ciwon gabobi, ciwon kai da kuma wahalar numfashi.
Ihekweazu ya ce ya zuwa ranar 24 ga watan Maris din 2021, jihohi guda bakwai sun bayar da rahoton barkewar nau’in cutar na H5N1 a jikin kaji da dama.
“Tuni aka kai jami’ain bayar da tallafin gaggawa daga NCDC da kuma Ma’aikatar Noma ta Tarayya zuwa jihohin Bauchi da Kano da kuma Filato.
“An dauki samfurin mutane 83 domin yin gwajin inda sakamakon 64 daga cikinsu, wato kaso 87.7 cikin 100 ya nuna suna dauke da cutar,” inji shi.
Shugaban na NCDC ya kuma ce tuni suka tura sakamakon binciken ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) kamar yadda ta bukata.