Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa cutar nan mai tsanani dake kama dabbobi ta murar tsintsaye ta sake barkewa a Najeriya.
Daraktan Sashen Kula Da Lafiyar Dabbobi da Yaki da Kwari na Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Kasa, Olaniran Alabi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
- Abin da ya sa Ganduje ya rufe masallacina —Sheikh Abduljabbar
- Ya mutu bayan dirowa daga bene mai hawa 7 a kokarin tserewa jami’an EFCC
Daraktan ya ambato Cibiyar Bincike Kan Lafiya Dabbobi ta Kasa dake Vom a jihar Filato wacce ya ce ita ce ta tabbatar da hakan a wani rahoto da ta karba ranar 29 ga watan Janairun da ya gabata.
Ya ce tuni ma’aikatar ta farfado cibiyoyin da za su fara kula da dabbobin da suka kamu a dukkan jihohi 36 na Najeriya.
“Cutar ta barke ne a wasu gidajen gona guda biyu inda dabbobi da dama ciki har da jiminoni, kaji, talo-talo, dawisu da kuma zabi suka kamu a jihar Kano.
“Bugu da kari, a cikin mako daya, an sake samun rahotannin barkewar cutar a wasu gidajen gona dake Jos a jihar Filato, wanda hakan ke nuna cewa cutar na ci gaba da yaduwa kenan,” inji sanarwar.
Cutar dai a tsakanin shekarun 2005 zuwa 2006 ta yi sanadiyyar asarar dabbobi da dama sakamakon kamuwa da ita, lamarin da ya tilasta kashe su domin takaita yaduwarta.