✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar Marburg ta kashe mutum 2 a Ghana

An killace mutum 34 saboda barkewar cutar Marburg a Ghana.

Hukumomin Lafiya a Ghana sun tabbatar da bullar cutar Marburg mai saurin yaduwa da ke da alaka kwayar cutar Ebola.

An tabbatar da bullar cutar ne bayan wani gwaji da aka yi wa wasu majinyata biyu da suka mutu a kasar kamar yadda BBC ya ruwaito.

Duka mutanen biyu wadanda suka fito daga yankin Ashanti sun rika nuna alamomin da suka hadar da gudawa, da zazzabi, da kuma amai.

An dai garzaya da majinyatan asibitin Ashanti kafin daga bisani su mutu kamar yadda Jakadan Hukumar Lafiya ta Duniya a Ghana, Dokta Francis Kasolohe ya tabbatar.

An dai daukin samfurin kwayoyin cutar da aka samu daga jikin mutanen biyu zuwa Cibiyar Bincike ta Pasteur da ke Senegal domin zurfafa bincike a cewar Dokta Francis Kasolohe.

In dai ta tabbata cutar Marburg ce, wannan ne karo na farko da kasar ke samun bullar cutar a cikinta, kuma kasa ta biyu a Yammacin Afirka bayan da a bara ta bulla a Guinea.

Hukumar lafiya ta duniya dai ta tura tawagar likitoci domin taimaka wa takwarorinsu na Ghana dakile yaduwar cutar a kasar.

Duk da cewa babu riga-kafin wannan cutar, ana bai wa wadanda suka kamu da ita shawarar su yawaita shan ruwa, yayinda likitoci ke kokarin lalubo hanyoyin maganceta.

A shekaraun bayan cutar ta bulla ne a kasashen DR Kongo, da Kenya, da Afirka ta kudu tare da kuma Uganda.

An killace mutum 34 a Ghana

Hukumomin lafiya a kasar Ghana sun killace mutum 34 saboda barkewar cutar Marburg wacce ke saurin yaduwa.

An killacen mutanen ne bayan sun yi mu’amala da mutunen da ake zargi cutar ta kashe.

Hukumomin sun ce suna sanya ido game da barkewar cutar Marburg a kasar, wacce aka bayyana samunta a wurare biyu a yankin Ashanti da ke kudancin kasar.

Jami’an daga hukumar lafiya ta duniya tare da hadin gwiwwar likitocin kasar suna fadada bincike tare da yin aiki tukuru domin ganin cutar ba ta yadu ba