Gwamnatin Kasar Ghana ta fara shirye-shiryen fara amfani da zinare wajen sayen mai maimakon amfani da Dalar Amurka kamar yadda taki yi a yanzu.
Tuni gwamnantin kasar ta yi yukurin samar da sabuwar dokar da za ta ba da damar yin amfani da wannan tsari.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabbin Kudaden Najeriya
- Gwamna ta yafe wa ’yan wiwi 47,000
Mataimakin Shugaban Kasar, Mahamudu Bawumia ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook ranar Alhamis.
Ya ce gwamnati za ta dauki wannan mataki ne don kyautata asusun ajiyarta na ketare da kuma karfafa wa kudin kasar.
Ya kara da cewa amfani da Dalar Amurka wajen sayen maye daga hannun ‘yan kasuwa na yi wa kudin kasar illa tare da tsananta wa ‘yan kasa tsadar rayuwa.
Duk da dai kasar ta Ghana na samar da danyen mai, amma ta dogara ne ga shigo da tataccen mai daga ketare tun bayan da aka lalata matatar man kasar a 2017.