Wata Kotu a kasar Ghana ta yanke wa wasu ’yan Najeriya biyu hukuncin kisa bayan samunsu da laifin garkuwa da kashe wasu ’yan mata hudu a kasar.
Samuel Udoetuk Wills wanda ya shiga rigar bafulatanin mutum da sunan Buba Muhammad da wani John Orji, sun yi garkuwa tare da kashe ’yan mata hudu a garin Tokoradi.
- An sace ’yan mata 3 ’yan gida daya a Kogi
- Gobara ta yi ajalin ’yan uwan juna hudu a garin Bida
- An fara yi wa fursunoni rigakafin cutar Coronavirus
Hukuncin da kotun ta yanke wa matasan biyu ya biyo bayan samunsu da laifin sacewa da kuma kashe Ruth Quayson, Priscilla Blessing Bentum, Priscilla Koranche da kuma Ruth Abekah wanda dukkaninsu basu haura shekara 18 ba.
Samuel da John sun yi garkuwa da ’yan matan hudu ne a Accra, babban birnin kasar kuma suka bukaci fansa ta makudan kudi.
A yayin da ’yan uwan wadannan mata ke tattaunawa a kan batun kudin fansar, Samuel ya shaida musu cewa shi Bafulatanin mutum ne wanda ya fito daga kasar Najeriya.
Ana tsakar haka ne ’yan uwan matan suka wallafa sunansa da hotunan matan a shafukan sada zumunta da zummar a taya su cigiya, lamarin da ya sanya jami’an ’yan sanda a kasar suka bazama wajen bincike.
Sai dai an yi rashin sa’a gabanin shigarsu hannu, Samuel da John suka kashe duk ’yan matan hudu bayan sun fahimci cewa babu ko asi da za su samu na kudin fansar da suke nema.
Yayin da Samuel ya shiga hannu, jami’an ’yan sanda sun gano cewa ba ya jin yaren Fulatanci ballantana kuma Hausa.