Mutum 816 sun rasu a sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihohi 22 da Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, a bana.
Da take bayar da alkaluman, Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce samun karuwar masu kamuwa da cutar ta sa ta bude cibiyoyin aikin gaggawan kula da masu cutar kwalara a ranar 22 ga Yuni, 2021.
“Daga ranar 1 ga Janairu zuwa 1 ga Agustan 2021, mutum 31,425 sun nuna alamar cutar kwalara, an tabbatar da kamuwar 311 daga cikinsu, wasu 816 kuma sun rasu a Abuja da wasu jihohi 22,” inji rahoton NCDC na ranar Litinin.
Jihohin da aka samu bullar cutar su ne: Binuwai, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sakkwato, Bauchi, da Kano.
Sai kuma Kaduna, Filato, Kebbi, Kuros Riba, Neja, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Kwara, Enugu, Adamawa, Katsina, Borno da kuma Birnin Tarayya, Abuja.
Hukumar ta ce duk da cewa Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Tarayya (NPHCDA) ta gudanar da allurar rigakacin cutar a Karamar Hukumar Bauchi ta Jihar Bauchi a watan Yuli, hakan ba shi ne zai kawo karshen matsalar cutar ba.
NCDC ta bayyana cewa cutar ana daukar kwayarta ce a cikin gurbataccen ruwa musamman a yankunan da ba sa samun isasshen ruwa mai tsafta.
“Yawan zubar da shara barkatai da yin bayan gida a fili suna barazana ga samuwar tsaftataccen ruwan sha da na amfani. Hakan ne kuma ke yada cututtuka irin kwalara da ake dauka daga gurbataccen ruwa.
“Idan har babu isassen ruwa da tsaftar muhalli, Najeriya za ta ci gaba da fama da bullar cutar da kuma asarar rayuka.
“Babbar mafita ita ce samar da tsaftataccen ruwan sha da sarrafa shara yadda ya kamata da kuma tsaftar muhalli da na abinci da jiki.
“Muna kara kira ga gwamnatocin jihohi da su dage wajen daukar matakan samar da tsaftatacce kuma isasshen ruwan sha tare da tabbatar da tsaftar muhalli a cikin al’ummomi,” a cewar NCDC.
Kwayar bakteriya mai suna Vibrio cholera ce take haddasa cutar ta kwalara wadda galibi ake dauka daga gurbataccen ruwa. Cutar mai sanya amai da gudawa tana kuma kisa.
Sauran alamomin cutar sun hada da raguwar ruwan jiki, wanda ke haddasa rauni da koda da firgici ko kuma mutuwa. Tana kuma sanya mutuwar jiki da bushewar fata.
NCDC ta roki jama’a da su dage wajen kula da tsaftar muhalli da kuma amfani da tsaftataccen ruwa ta hanyar tafasawa da kuma adanawa yadda ya kamata a wuri mai tsafta.
Ta kuma yi kira da a guji yin bayan gida barkatai a fili sannan a rika wanke hannu a-kai-a-kai.
Hukumar ta kuma bukace su da su gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da suka ji daya daga cikin alamomin cutar.